Kunji wata kuma: Banyi imani da 'Bible' ba saboda cike yake da labaran gizo da koki - Kemi Olunloyo

Kunji wata kuma: Banyi imani da 'Bible' ba saboda cike yake da labaran gizo da koki - Kemi Olunloyo

- Kemi Olunloyo ta bayyana rashin yaddarta dangane da littafin Bible, inda tace bata yadda dashi ba kuma bata karanta shi ma gaba daya

- Ta kuma kara da cewa bikin kirsimeti da ake yi ranar 25 ga watan Disamba bashi da alaka da kiristoci, hasali ma Annabi Isa ba ranar aka haife shi ba

- Ta ce da ace mutane suna da irin halinta na rashin tsattsauran ra'ayi akan addini da kowa ya zauna lafiya a duniyar nan

Kemi Olunlayo ta nuna rashin yaddarta akan littafin Injila wato 'Bible' a wani sabon rubutu da ta wallafa a shafinta na sada zumunta. Matar ta dauki lokaci domin tayi bayani dangane da yadda ta dauki littafin 'Bible' din inda ta bayyana cewa cike yake da labaran kanzon kurege.

Sannan kuma ta bayyana cewa bikin kirsimeti da ake yi bashi da alaka da Kiristoci, saboda yanzu babu inda ba ayin wannan biki a duniya. Ita dai Miss Olunloyo tayi suna a shafukan sada zumunta wajen tunzura mutane akan irin rubutun da take wallafawa wadanda suke sanya mutane da yawa cikin rudani.

KU KARANTA: An dakatar da wata budurwa ma'aikaciyar banki da tayi zina da maza sama da 200, bayan ta yi musu alkawarin nema musu aiki

Ga rubutun da ta wallafa dangane da maganar da tayi na cewa bata yadda da littafin 'Bible' ba:

"Mutane da yawa a shafin sadarwa suna tambayata akan yadda aka yi na san da Annabi Isa da Allah, idan ba ta bangaren 'Bible' ba, wannan tambayar shirme ce.

"Kuma amsar tambayarku ita ce na san sune ta hanyar wani malamin makarantar mu da yake bamu labari. Ni ban yadda da Bible ba kuma bana karanta shi. Bama zan kara taba shi ba har rayuwata ta kare, saboda cike yake da labaran karya.

"Allah bai ce dole sai mun bauta mishi ta hanyar karanta Bible ba, ko kuma ta hanyar Fasto ba. Inda ace mutane duka halinsu daya dani ba su da tsattsauran ra'ayi akan addini da kowa ya zaunaa lafiya a duniyar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel