Akalla yan Najeriya 10,000 ke karuwanci a kasar Burkina Faso

Akalla yan Najeriya 10,000 ke karuwanci a kasar Burkina Faso

Jakadiyar Najeriya a kasar Burkina Faso, Ramatu Ahmed, ta ce akalla yan matan Najeriya 10,000 ke aikin karuwanci a kasar Burkina Faso.

Wannan magana ya biyo bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar domin halartan taron kungiyar ECOWAS a karshen makon da ya gabata.

Ramatu Ahmed ya bayyana hakan ne a wani hira da ta tayi da kamfanin dillancin labarai NAN a Ouagadougou a ranar Litinin inda ta ce ana amfani da kananan yara wajen karuwanci a kasar musamman a birnin kasar.

Ramatu ta ce kawo yanzu, an mayar da yan Najeriya 200 gida.

A cewarta, yawancin yan matan da aka yiwa alkawarin aikin yi a kasar Burkina Faso da Turai ba su son komawa gida.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Adamawa da Sanata Elisha Abbo

Ga kalamanta: "Yadda ake safarar mutane a nan kasar Burkina Faso babban abin damuwa ne ga ofishin jakadancin saboda yanzu, akwai akalla yan matan Najeriya 10,000 da aka shigo da su kasar Burkina Faso a matsayin karuwai."

"Hakazalika yawancin yan matan kananan yara ne; yawancinsu sun daina karatu sai yawace-yawacen karuwanci a Burkina Faso."

A ranar Asabar Shugaba Muhammadu Buhari ya samu kyakkyawan tarba yayinda ya dira Ouagadougou, babbar birnin kasar Burkina Faso inda yaje halartan taron kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS kan yaki da rashawa.

Shugaba Buhari ya tafi Burkina Faso a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, 2019 tare da gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu; Niger, Abubakar Bello da Ogun, Dapo Abiodun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel