Da duminsa: Sarkin da aka kwancewa rawani a jihar Zamfara ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar PDP

Da duminsa: Sarkin da aka kwancewa rawani a jihar Zamfara ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar PDP

Tsohon sarkin Bakura a jihar Zamfara, Hassan Marafa, ya zama sabon mataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Zamfara.

Hassan marafa, ya samu nasarar hakan ne a zaben jam'iyyar da ya gudana ranar Litinin a a Gusau, babbar birnin jihar.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Aliyu Mamuda Shinkafi, ne ya nada Hassan matsayin sarkin Zamfara a 2010 amma tsohon gwamna, AbdulAziz Yari, ya tsigeshi kuma ya maye gurbinsa da mai ci yanzu, Bello Sani.

Marafa zai zama mataimaki ga shugaban jam'iyyar, Ibrahim Mallaha, wanda ya aka sake zabensa a zaben karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu.

Hakazalika, Hamisu Modomawa, ya zama Sakataren jam'iyyar inda tsohuwar jagorar mata, Ai Maradun, ta zama jigon yankin yammacin Zamfara.

Sauran shugabannin jam'iyyar sune Sani Sada, Isa Maigemu, da Sule Anka.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Adamawa da Sanata Elisha Abbo

A bangare guda, ranar Litinin, 16 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane takwas cikin majalisar masu bashi shawara kan harkan tattalin arziki.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto daga hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, inda ya bayyana cewa wannan sabuwar kwamiti da Buhari ya nada za su rika magana da shi kai tsaye ba tare da wani dan aike ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel