Allah kare: Jahohin Arewa guda 8 dake fuskantar mummunan barazanar ambaliyan ruwa
Hukumar kimiyyar ruwa ta Najeriya, NIHSA ta bayyana cewa samun karin ruwa a tafkin Benuwe zai kawo babbar barazana musamman ga jahohin Adamawa, Taraba da Benuwe ta wajen samun mummunan ambaliya, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Shugaban hukumar, Clement Nze ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba inda yace an samu karin ruwa daga kasashen Afirka zuwa Najeriya.
KU KARANTA: Yansanda sun halaka gungun miyagu masu garkuwa da mutane a jahar Kogi
“A yau dinnan an samu karin ruwa daga tafkunan kasashen Afirka guda 6 cikin kasashe 8 dake makwabtaka da Najeriya, kuma duk ruwan zasu taru ne a tafkin Benuwe, wanda hakan zai kawo ambaliyan ruwa a jahohi guda 10.
“Jahohin sun hada da Kebbi, Nassarawa, Neja, Kogi, Kwara, Taraba, Adamawa da Benuwe, akwai yiwuwar samun ambaliya a Edo, Anambra, Delta, Ribas da Bayelsa.” Inji shi.
A wani labarin kuma, gungun miyagu yan bindiga sun kai wata mummunan farmaki a kauyen Katsira Tsauna dake cikin karamar hukumar Sabon Birni inda suka halaka wasu matasa guda uku ba laifi fari ba laifin baki.
Miyagun sun kai harin ne da yammacin Asabar, 14 ga watan Satumba a kan babura guda 5 goyon bibbiyu, inda baya ga kashe matasan, sun kuma jikkata wasu mata guda uku, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a babban asibitin garin Sabon Birni.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng