Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

Ko kunsan dalilin kama mawaki Naziru M. Ahmad?

- Kama mawaki Naziru M. Ahmad da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sake tado kurar rikicin siyasa

- Wasu na kallon hakan da siyasa ce zalla ba laifin da ake zarginsa ba

- Amma kuma Afakallahu yace karan tsaye da mawakan ke yi wa hukumar tace fina-finai ce ta jawo hakan

Cafke mawaki Naziru M. Ahmad da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi a yammacin ranar Laraba ya sake tado kura kan rikicin siyasar da ke faruwa a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaidawa BBC cewa sun kamasa ne "Saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Mawakin ya musanta zargin da ake masa na mallakar dakin gudanar da waka a gidansa.

Sai dai sanannen daraktan fina-finai kuma dan uwan mawakin ya shaidawa BBC Hausa cewa gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama Dan uwansa ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar.

"An kama Naziru ne saboda fitar da kundin waka da ya yi mai suna 'Gidan Sarauta' da kuma 'Sai Hakuri'," inji Saira.

KU KARANTA: Kasar Afirka Ta Kudu za ta turo wakilai na musamman Najeriya

Hasalima kundin wakokin sun fita ne shekaru hudu da suka gabata.

A ranar Juma'a dai an bada belin Naziru akan kudi naira 500,000 , fasfo dinsa na tafiye-tafiye, shaidu uku ma'aikatan jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune.

Sai dai Jaridar Daily Trust ta ambato cewa shugaban hukumar tace fina-finai, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya musanta zargin cewa siyasa ce ta sa ake cin zarafin mawakan. A cewarsa mawakan sun keta dokokin hukumar tace fina-finan ne.

Sanannen abu ne cewa Naziru shi ne Sarkin wakar Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Sarkin da ya dade yana kai ruwa rana da gwamnatin jihar wanda hakan ya kawo rabuwar masarautarsa da gwamnatin ta yi har gida biyar.

Kazalika, mawakin fitaccen Dan kungiyar kwankwasiyya ne, wato bangaren siyasar jam'iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano, wacce madugu Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Aminu Saira na ganin cewa kama Naziru bai rasa nasaba da siyasa ba , domin kuwa idan Dan uwan nasa ya yi waka, 'yan kasuwa take sayarwa. Don haka su yakamata a tuhuma. Kazalika kamfanin da yake buga wakoki na Aminu Saira ne ba Naziru ba. A don haka kuwa idan akwai matsala a wakokinsa, Saira yakamata a kama ba Naziru ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel