Shuwagabannin kasashen Afirka Ta Yamma sun aminta da kashe makudan kudi don kawo karshen ta'addanci

Shuwagabannin kasashen Afirka Ta Yamma sun aminta da kashe makudan kudi don kawo karshen ta'addanci

- Shuwagabannin kasashen Afirka ta yamma sun amince da kashe dala biliyan daya don kawo karshen ta'addanci a yankin

- Sunyi yarjejeniyar ne a wajen taron kungiyar cigaban tattalin arzikin Afirka ta yamma da aka gudanar a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shuwagabannin akan dagewa wajen kawo karshen rashin tsaro da ke addabar yankin

Shuwagabannin kasashen Afirka ta yamma sun aminta da kashe dala biliyan daya don yaki da rashin tsaro da ya addabi yankin.

Sunyi wannan yarjejeniyar ne a wajen taron kungiyar cigaban tattalin arzikin Afirka ta gamma da aka gudanar don kawo karshen ta'addanci a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso a ranar Asabar.

Kudaden za a kashesu ne don wajen shiri na musamman don yaki da ta'addanci a yankin.

Kamar yadda suka bayyana, wa'adin wannan shirin zai fara ne daga shekarar 2020 zuwa 2024.

Za a kashe kudaden ne wajen kara inganfa sojin da ke yaki da ta'addanci a yankunan.

A wajen taron, Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Afirka ta yamman su hada kawunansu don yakar 'yan ta'addan da suka zamewa yankin karfen kafa.

Ya ce, "A wannan dalilin ne ya sa dole kasashen su yi amfani karfinsu, dukiyoyinsu da tunaninsu wajen horarwa tare da samarwa sojin makamai don yaki da ta'addanci."

KU KARANTA: Toh fah: NFIU ta nemi bayanai kan asusun ajiyar bankin wasu alkalai da 'yan majalisa

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ba da shawarar cewa kada su kuskura su bar 'yan ta'addan su tarwatsa yankin.

"Yankinmu ya samu cigaba mai yawa, kada mu bari 'yan ta'addan su watsa mana yankin, su sanyawa mutanenmu tunanin cire rai daga ni'imomin da muka mallaka."

Shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, Jean-Claude Kassi Brou, ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan muhimmin taro alama ce ta hadin kai tsakanin kasashen domi. Yaki da matsalar da ke damun yankin.

A watan Yulin wannan shekarar ne Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ana samun yaduwar masu yaki da sunan addini a Afirka ta Yamma, don haka akwai bukatar kara kaimi wajen yakarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel