Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

- Wata mace musulma, Zulfalt Suara tayi nasarar lashe zabe a Nashville da ke kasar Amurka lamar yadda alkalluman zabe suka nuna

- Suara ta fuskanci kalaman kiyaya ga musulunci daga wurin mutane da dama lokacin kamfen dinta amma duk da hakan akwai masu son ta

- Zulfat ta ce sakamakon zaben ya nuna cewa Nashville gari ne mai tattare da mutane daban-daban

Wata musulma bakar fata a kasar Amurka ta sake lashe zaben kujerar wakiliya kamar yadda sakamakon zaben ke nuna wa. Idan Hukumar Zabe ta tabbatar da sakamakon zaben, Zulfat Suara za ta zama mace musulma ta farko da aka zaba a majalisar Nashville.

Fox17 ta ruwaito cewa Suara ta yi wa magoya bayan ta jawabi a daren ranar Alhamis 12 ga watan Satumba inda ta nuna cewa tana sa ran cewa ita za ta lashe zaben.

Saura wacce kwararriyar Akanta ce a Kwallejin Lafiya ta Meharry ta fuskanci hare-hare na kyamar musulmi yayin yakin neman zaben ta amma hakan bai sa ta karaya ba inda ta cigaba da neman kuri'u daga mabiya addinai daban-daban.

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

Yayin yakin neman zaben ta ta mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi kudi da ilimin makarantun gwamnati.

A wani hira da aka yi da ita, ta ce idan ba tayi nasara ba za ta koma rayuwar ta na 'yar gwagwarmaya.

"Ya zama dole in fada wa kai na cewa idan banyi nasara ba zan koma in cigaba da rayuwa ta na gwagwarmaya. Sai naji magoya baya na sunyi ihu hakan yasa na ke ganin zan yi nasara," inji ta.

Sakamakon zaben ya nuna cewa Suara ta dara wanda ke biye da ita, Sheri Weiner da kuri'u 2,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel