Nau'ikan abinci 10 da bai dace a ajiye su cikin firinji ba

Nau'ikan abinci 10 da bai dace a ajiye su cikin firinji ba

Firinji na'ura ce da ake amfani da shi domin adana kayan abinci da ababen sha ta hanyar sanyaya su. Sai dai akwai wasu nau'oin abinci da bai dace a rika sa su cikin firinji ba domin sanyi na iya lalata su ko sauya musu dandano.

Ga wasu daga cikin irin abincin da bai dace a saka a firinji ba.

1. Burodi

Burodi ya kanyi saurin bushe wa ko ya lalace indan an sa a firinji kuma ba a bukatar hakan musamman idan ana son amfani da shi cikin 'yan kwanaki. Ya fi dace wa a ajiye shi a wuri mai inuwa kuma mara lema.

2. Tumatur

Sanyi ya kan lalata fatar jikin tumatur ya sanya tayi laushi da kuma fara fitar da ruwa. Saka tumatur a firinji kuma yana sauya dandanon su. Wurin da ya fi dacewa a ajiye tumatur shine a fili a kitchen. Idan kana da tumaturi da yawa, sai ka soya su ko tafasawa ko sakawa a gwangwani kamar na kamfani.

3. Dankali

Ajiye dankali cikin firinji yana da hatsari sosai ga lafiyar mutum. Idan an ajiye dankali a firinji, sunadarin starchi da ke cikinsa na sauyawa ya zama sukari, idan an dafa ko soya dankalin, sukarin zai hade da amino acid asparagine ya zama wani sinadari mai guba, acrylamide da ke iya kawo matsaloli a tsokar na hanyoyin isar da sako na jikin dan adam.

DUBA WANNAN: An bawa wani mai sukar gwammatin Buhari mukami a gwamnati

4. Zuma

Idan an ajiye shi cikin yanayin sanyi, zuma ya kan fara daskarewa, a maimakon a same shi cikin yanayinsa na ainihi.

5. Albasa

Yanayin da yafi dacewa a ajiye albasa shine cikin wuri mara danshi kuma tare da iska yana zagayawa. Albasa na dauke da sinadarin starchi saboda haka ajiye su a firinji na lokaci mai tsawo zai sa su duri ruwa su lalace. Sai dai idan an yanka albasa, ana iya rufe sauran cikin mazubi sannan a saka a firinji.

6. Man zaitun

Ajiye man zaitun cikin firinji ya kan sa shi za dushe kuma ya fita yanayinsa. Ya fi dacewa a ajiye shi a daki ko cikin wurin ajiya a kitchen inda rana ba zai taba shi ba a maimakon saka wa a firinji.

7. Shayin Coffee

Coffee yana daukan kamshin duk wani abu da ke kusa dashi saboda haka saka shi a firinji sai sauya dandanonsa. Kamata ya yi a ajiye shi cikin mazubi mai murfi kuma a guji ajiyewa inda rana zai taba shi.

8. Cakulet (Chocolate)

Saka cakulet a cikin firinji ya kan sauya dandano da launin ta saboda danshi da ke firinjin. Cakulet mai dandanon cocoa butter kuma ya san dauki kanshin abincin da ke kusa da shi saboda haka zai fi dacewa a ajiye cakulet a cikin mazubi mai murfi da iska ba zai shiga ba.

9. Man Salad

Man salad suna dauke da maiko saboda haka ya fi dacewa a ajiye su a wurin ajiye a kitchen ba tare da an saka a firinji ba.

10. Cake

Ajiye cake cikin firinji zai sauya dandanonsa musamman idan an masa ado da sukari. Kamata ya yi a ajiye shi cikin mazubin ajiye cake har zuwa lokacin da za ayi amfani da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel