Dan sanda ya kashe wani dan-acaba a jihar Jigawa

Dan sanda ya kashe wani dan-acaba a jihar Jigawa

Wani dan sanda ya kashe wani mutum mai acaba da babur a jihar Jigawa dake Arewa maso yammacin Najeriya a dalilin saba dokar tuki da yayi.

Adamu Idris, Shugaban kungiyar masu acaba na jihar Jigawa ne ya bada tabbacin kisan Yunusa Isma’il mai shekaru 35 ranar Litinin a Dutse babban birnin jihar.

KU KARANTA:Manufar Buhari game da Najeriya ta bambanta da ta Osinbajo – Shehu Sani

Majiyar Channels Tv ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar masu acaban ne ya ce jami’in ‘yan sanda ne ya doki mai acaban da sanda saboda ya keta dokar hanya.

Idris ya cigaba da cewa, wannan al’amarin bai yiwa ‘yan kungiyarsa dadi ba. Abinda ya janyo zanga-zanga tare da farfasa motar daya daga cikin jami’an ‘yan sandan.

“Nan take jami’in dan sandan da yayi kisan ya bar wurin yayin da ya ga masu babur sun nufo wurin da yake.” Inji Idris.

Hukumar ‘yan sandan jihar ta gaskata aukuwar wannan lamari. Abdu Jinjiri, kakakin rundunar ‘yan sandan Jigawa ya shaidawa Channels TV cewa ‘yan sandan da suka gudanar da aiki a kan hanyar Ibrahim Aliyu bypass sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Amma sai dai ba su fadi cewa an doki dan acaban da sanda ba. A cewar hukumar ‘yan sandan jihar: “Ismail ya hangi motar ‘yan sanda ne sai yayi kokarin juyawa domin ya gudu kawai sai ya fadi a wurin.

“An yi gaggawar kai shi asibiti a cikin motar ta ‘yan sanda amma daga bisa ni aka sanar cewa rai yayi halinsa.”

Jinjiri ya ce sun tattara wannan badakkala zuwa hedikwatar ‘yan sanda dake Abuja saboda sarkakiyar dake cikinta.

https://www.channelstv.com/2019/09/13/policeman-reportedly-kills-motorcyclist-in-jigawa/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel