Zaben jahar Kogi: Sanata Dino Melaye ya yi watsi da tayin mukami da PDP ta yi masa

Zaben jahar Kogi: Sanata Dino Melaye ya yi watsi da tayin mukami da PDP ta yi masa

Wakilin mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa Sanata Dino Melaye ya yi fatali da tayin wani muhimmin mukami da jam’iyyar PDP ta yi masa a kokarinta na kwace jahar Kogi daga hannun jam’iyyar APC.

Legit.ng ta ruwaito jam’iyyar PDP ta yi ma Dino Melaye tayin mukamin shugaban yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar Kogi na jam’iyyar PDP a zaben gwamna da zai gudana a watan Nuwambar shekarar 2019.

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya yi karin haske game da harbe harben da aka yi a gidansa

Sai dai a wata sanarwar da Melaye ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya bayyana cewa baya bukatar wannan mukami, don ya yi fatali da shi, amma duk da haka yana yi ma jam’iyyar PDP fatan alheri a zaben.

“Bari na bayyana da kyau cewa na yi watsi da mukaman jagoran majalisar yakin neman zaben gwamnan jahar Kogi na jam’iyyar PDP, kuma ina yi ma jam’iyyar PDP fatan alheri. Idan har aka tauye gaskiya, ba za’a samun zaman lafiya ba.” Inji shi.

Idan za’a tuna bayan kammala zaben fitar da gwani na dan takarar gwamnan jahar Kogi na jam’iyyar PDP, shugaban zaben, gwamnan jahar Adamawa Umaru Fintiri ya sanar da Injiniya Wada Musa a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 748, yayin da Melaye ya samu 70.

Sai dai an samu yamutsi sosai yayin da ake gudanar da kidayan kuri’un, inda a daidai wannan lokaci wasu gungun yan bindiga suka kutsa kai cikin farfajiyar filin wasa na garin Lokoja inda ake gudanar suka bude wuta, irin harbin mai kan uwa da wabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel