Assha: Wata mata ta kashe kanta saboda mijinta ya hanata shan sigari

Assha: Wata mata ta kashe kanta saboda mijinta ya hanata shan sigari

Wata mata ‘yar kasar India ta kashe kanta saboda mijinta ya hanata shan sigari. Poonam sunan matar kuma shekarunta 26 inda ta fito daga garin Punjab.

Matar dai ta fusata ne a sanadiyar hanata shan sigari da mijin nata yayi, lamarin da har ya sanya Poonam ta rataye kanta saboda takaici.

KU KARANTA:Kotu ta dakatar da majalisar dokokin Najeriya daga cusa kai cikin lamuran majalisar jihar Edo

Wannan al’amarin dai ya auku ne a daren Litinin 9 ga watan Satumba, 2019 bayan da mijin ya ki barin matar ta shan sigarin.

Abinda kuwa ya biyo baya shi ne Poonam ta shiga daki ta rataye kanta, ba a tashi sanin halin da take ciki ba sai washe garin Talata 10 ga watan Satumba kenan.

Nan take mijinta ya sanar da ‘yan sanda cewa ga halin da matarsa take ciki, inda aka zo aka dauki matar aka kai gawarta asibiti domin binciken dalilin mutuwarta.

Vinod wanda shi ne mijin matar ya bada labarin musabbin mutuwarta, inda ya ce tayi matukar sabawa shan tabar sigarin mai suna ‘Gutka’ yadda har ya zame mata jiki idan ba ta sha ba ba zaman lafiya.

Kamar yadda mijin ya bada labara, da yammacin Litinin ne matar tasa ta nemi ya bido mata tabar inda shi kuma yaki kasancewar ba ya kaunar shan tabar da matar ke yi.

Kafin mijin ya farga ashe matar tasa ta fada wani daki inda ta rataye kanta sai dai kawai ya shigo ya tarar da gawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel