'Yar Najeriya ta zama 'yar majalisa a kasar Canada

'Yar Najeriya ta zama 'yar majalisa a kasar Canada

An zabi haifaffiyar Najeriya, Uzoma Asagwara, a matsayin 'yar majalisar tarayya mai wakilcin mazabar Manitoba a kasar Canada.

Nasarar da Asagwara tayi a karkashin jam'iyyar NDP (New Democratic Party), ta kasance bakar fata ta farko a tarihin kasar Canada da a ka zaba a matsayin 'yan malajisar tarayya mai wakilcin mazabar Manitoba.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai mai tushe a kasar Canada wato CBC ya ruwaito, Asagwara ta kasance cikin jerin bakaken fata uku a tarihi da aka taba zaba a matsayin 'yan majalisar kasar tun yayin kafuwar majalisarta shekaru 150 da suka gabata.

A yayin da ta ke zantawa da manema labarai a ranar Talata 10 ga watan Satumba, Asagwara ta nemi dukkanin zababbun shugabanni a mazabarta suka kasance magartan jakadu da za su wakilci al'umma da kuma yankin baki daya.

Rahotanni sun bayyana cewa, gabanin nasararta a zaben kasar da aka gudanar, Asagwara ta kasance ma'aikaciyar lafiya a wani asibiti masu cutar hauka kuma mai fafutikar kare hakkin dan Adam a birnin Winnipeg.

KARANTA KUMA: Kotun zabe ta tabbatar da nasarar 'yan majalisar Kano Jibrin da Gaya

Uzoma ta yi godiya da jinjina ga dukkanin wadanda suka goyo mata baya tun gabanin nasarar da tayi a zaben kasa.

Ana iya tuna cewa, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sabon Firaiministan Birtaniya, Borris Johnson, ya zabi wata 'yar Najeriya, Olukemi Olufemi Badenoch, a matsayin karamar ministan kula da yara da kuma iyalai a kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel