Tashin hankali: Dalibi na biyu ya rasa ransa sakamakon harbin 'yan sanda a Jami'ar Ekiti

Tashin hankali: Dalibi na biyu ya rasa ransa sakamakon harbin 'yan sanda a Jami'ar Ekiti

- Dalibi ya sake mutuwa sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi a zanga-zangar lumanar da daliban jami'ar tarayya ta Oye Ekiti suka yi

- Amma hukumar 'yan sanda ta musanta inda tace zance ne mara tushe balle makama

- Tuni dai hukumar makarantar ta rufe makarantar ba tare da sanar da ranar dawowa ba

Jaridar Premium Times ta bada rahoton yadda dalibai biyu suka rasa rayukansu sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi yayin zanga-zangar da daliban jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti suka yi.

'Yan sanda sun ce rahoton bashi da tushe balle makama kuma babu jami'in da yayi harbi yayin kwantar da tarzomar.

Ganau ba jiyau ba sun tabbatarwa jaridar Premium Times yadda 'yan sandan suka yi harbi don kare tawagar uwargidan gwamnan jihar Ekiti, Bisi Fayemi.

A yau Laraba dai gwamnatin jihar ta ce tana jiran ji daga bakin hukumar makaranta.

Amma kuma gwamnatin tayi shiru akan cewa 'yan sandan sunyi harbi ko basu yi ba kuma waye wanda ya basu damar harbin.

Kisan ya faru ne bayan da dalibai masu zanga-zangar suka tare tawagar uwargidan gwamnan don bayyana mata damuwarsu.

KU KARANTA: Kotun zabe: Gwamna Dapo Abiodun da Adekunle Akinlade za su san makomarsu ranar Asabar

A dazu mun samu rahoton mutuwar daya daga cikin daliban da ke kwance magashiyyan a asibiti. Dalibin dan shekara ta uku a jami'ar mai suna Okonofua Joseph ya rasu ne yau Laraba bayan da Oluwaseyi Kehinde, dalibin shekarar farko a jami'ar ya rasu a jiya Talata.

Matakin da makarantar ta dauka ya bayyana ne tun a daren yau Laraba, inda hukumar makarantar ta tura sakon kar ta kwana ga daliban akan rufe makarantar. Sun bukaci daliban da su bar cikin makarantar harda harabarta zuwa karfe 10 na safiyar Laraba.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Ikechukwu ya musanta mutuwar daliban. Ya bayyana cewa an samu makami a tare da daliban masu zanga-zangar. A don haka ne ake zargin wasu bata-gari sun shiga cikin daliban don tada tarzoma.

"Daliban masu zanga-zangar sun tare tawagar matar gwamnan jihar. A don hakane 'yan sanda suka fito don bude hanyar. Lokaci kadan suka koma kai hari ga motocin tawagar tare da hantarar 'yan sandan. Akwai yuwuwar bata-gari sun shiga cikin daliban don tada hankula."

"Ana cigaba da bincike don gano bata-garin kuma zasu fuskanci fushin hukuma," Ikechukwu ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel