'Yan sanda sun kashe mana mambobi 15, sun cafke 64 yayin tattakin Ashura - IMN

'Yan sanda sun kashe mana mambobi 15, sun cafke 64 yayin tattakin Ashura - IMN

Kungiyar mabiya akidar shi'a ta Najeriya wadda kuma ake kira da IMN (Islamic Movement of Nigeria), ta ce jami'an 'yan sanda a fadin kasar nan sun kashe mata mambobi 15 a yayin tattakin Ashura da ta gudanar a ranar Talata.

IMN ta yi ikirarin cewa jami'an 'yan sanda sun kashe mambobinta yayin tattakin Ashura da ta gudanar a jihohin Bauchi, Kaduna, Gombe, Sakkwato da kuma Katsina.

Mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa, ya shaida wa manema labarai na jaridar The Punch cewa, an kashe mambobin IMN 3 a jihar Kaduna da raunata 10, a yayin da kuma a kashe wasu shida a jihar Bauchi.

Sauran sun hada da mutum biyu da aka kashe a yankin Illela da Goronyo a jihar Sakkawato da kuma uku a Gombe, sai kuma mutum daya a Malumfashin jihar Katsina.

Kungiyar ta ce ta gudanar da tattakin ta salin alin ba tare da wani tashin hankali ba a biranen Abuja, Jos, Kebbi, Minna, Lafia, Yola, Gusau, Zaria, Kano, Jalingo, Damaturu, Hadejia da kuma Potiskum.

Sai dai hukumar 'yan sandan Najeriya ta musanta wannan zargi da cewar ba bu ko mutum guda da kashe, inda ta bayar da tabbacin cafke mabiya akidar shi'a a 28 a jihar Bauchi, da kuma 36 a kananan hukumomin Dutsinma, Malumfashi da kuma birnin Katsinan Dikko.

KARANTA KUMA: An cafke matashin da ya cilla jariri cikin ruwa a jihar Neja

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Talata 10 ga watan farko a shekarar Musulunci, mabiya akidar shi'a a Najeriya, sun gudanar da tattakin tunawa da kuma nuna juyayin mutuwar Imam Hussaini ibn Ali, wanda aka kashe a yayin yakin Karbala shekaru fiye da dubu daya da suka gabata.

Ilahirin mabiya akidar shi'a a fadin duniya na gudanar da wannan tattaki domin nuna bakin cikin su a wannan rana ta 10 ga watan Al-Muharram, a kan mutuwar Imam Hussain wanda ya kasance jikan Manzon Tsira, Annabi Muhammad (Salallahu Alaihi Wasallam).

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel