Mutum 31 ne suka rasa ransu sai 100 da suka samu raunika a ranar Ashura

Mutum 31 ne suka rasa ransu sai 100 da suka samu raunika a ranar Ashura

- Ma'aikatar lafiya ta kasar Iraqi ta bayyana cewa mutane 31 ne suka rasa rayukansu inda 100 suka samu raunika

- Musulmai mabiya aqidar Shi'a sunyi tattaki cikin birnin Karbala inda suke zanar kansu da kaca

- Gwamnatin kasar Iraqi dai ta bada hutun ranar Ashura a kasar tare da tura dubban soji da 'yan sanda don wanzar da zaman lafiya

A ranar Talata ne ma'aikatar lafiya ta kasar Iraqi tace an kashe mutane 31 kuma wasu mutane 100 sun samu raunika a yayin murnar Ashura a birnin Karbala.

Ma'aikatar ta ce mutane 10 daga cikin wadanda suka samu raunin na cikin matsanancin hali.

Kamar yadda cibiyar yada labarai ta kasar ta sanar, akwai yuwuwar karuwar yawan mace-macen da kuma masu samun raunikan.

KU KARANTA: Mabiya El-Zakzaky sun kai mana hari da gwafa amma ba su kashe su ba - 'Yan sanda

Dubban musulmai mabiya aqidar Shi'a ne suka taru a masallacin don bikin tunawa da rasuwar Imam Hussein, daya daga cikin jikokin Annabi Muhammad.

Sunyi tattaki ta cikin birnin Karbala, suna zanar bayansu da kirjinsu da kaca tare da kuka yayin da jini ke ambaliya daga jikinsu da fuskokinsu.

Miliyoyin musulmai mabiya aqidar Shi'a a kasar Iraq dai sun saba yin hakan a ranar Ashura. Ranar kuwa tana fadawa ne a duk 10 ga watan Muharram, watan farko na musulunci.

Gwamnatin kasar Iraqi sun bada hutun ranar Talatan a duk fadin kasar tare da tura dubban sojin kasar da 'yan sanda don wanzar da zaman lafiya yayin makokin.

Ashura a wajen sauran musulmai kuwa rana ce da Ubangiji ya tserar da Annabi Musa daga mutanen Fir'auna.

Amma kuma ga mabiya aqidar Shi'a, sam ba hakan bane. Rana ce ta tuna rasuwar Hussein a yakin Karbala a kasar Iraqi a shekarar 680 bayan mutuwar Annabi Isah.

An dade da haramta wannan biki a Iraqi na tsawon shekaru karkashin mulkin Saddam Hussein.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel