Na hallaka yayana saboda marowaci ne, ya fiye bukulu - Matashi

Na hallaka yayana saboda marowaci ne, ya fiye bukulu - Matashi

Hukumar yan sandan jihar Ekiti ta bayyana cewa ta damke wani matashi dan shekara 24 mai suna, Ebenezer Olurunleke, kan zargin kisan yayansa tare da wasu abokansa guda uku.

Kwamishanan yan sandan jihar, Asuquo Amba, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce matashin wanda dan asalin jihar Kogi ne ya kashe dan'uwansa da wuka da skoondireba a garin Okeila, birnin Ado Ekiti, a ranar 29 ga watan Agusta kuma ya sace da babur dinsa da wasu kayayyaki

Yayinda yake tona asirin abinda ya faru, Olurunleke ya bayyana cewa shi da abokansa ne suka kashe yayan.

KU KARANTA: Kotu ta fitittiki babban Sanatan APC, ta ce PDP taci zaben

Ya ce abinda suka yi nufin yi kawai shine su tayashi kwace kudin yayan saboda marowaci ne.

Yace: "Ban shiga dakin tare da su ba amma lokacin da na ga alamun cewa sun caka masa wuka kuma yana iwu, sai na shiga domin in cecesa amma sai ya cije ni, ya guntule min dan yatsa."

"Daga baya abokan nawa suka kawo min hari gidana. Sun bukaci sayar da babur (da na sace) amma na kiya."

"Na fara tunanin kai kara ofishin yan sanda amma yan sanda suka damkeni da babur din."

Kwamishanan yan sandan yace za'a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel