Ana siyasantar da batun tsaro a Najeriya - Buhari ya magantu a kan halin da kasa ke ciki

Ana siyasantar da batun tsaro a Najeriya - Buhari ya magantu a kan halin da kasa ke ciki

Shugaban kasa, Muhamadu Buhari, ya yi zargin cewa ana siyasantar da batun tsaro a Najeriya 'babu gaira, babu dalili', tare da bayyana cewa alakaluma sun nuna cewa akwai raguwar kalubalen tsaro daga shekarar 2015.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar shugabanni masu rajin tabbatar da tsaro a fadarsa dake Abuja.

Shugaban kasar ya ce duk yadda wasu jama'a suka yi kokarin tauye tarihi, alkaluma zasu fitar da gwamnatinsa daga duk wani zargi.

"Alkaluma sun nuna halin da muke ciki ta fuskar tsaro a shekarar 2015, da halin da muke ciki yanzu, da kuma inda muka dosa," a cewar shugaba Buhari.

Buhari ya ce dukkan nasarorin da gwamnatinsa ta samu daga shekarar 2015 zuwa yanzu a bayyane suke tare da bayyana cewa, "hatta nasarorin da muka samu a bangaren tsaro a bayyane suke duk da an siyasantar da batun."

Ya jinjina wa kokarin shugabannin kungiyar na shirya wani taron shugabannin kasashen Afrika da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna kalubalen tsaro da sauran wasu muhimman batutuwa.

Shugaban kungiyar, Mista Mamman, tsohon janar din soji da yanzu ke rike da sarautar gargajiya, ya ce, "mun zo wurinka ne saboda mun gamsu cewa gwamnatinka na da shirin kawo karshen kalubalen tsaro a kasar nan.

"Kafin hawanka mulki a shekarar 2015, kungiyar Boko Haram ta kwace iko da wasu sassan kasar nan.

"Jazircewar ka da kuma kokarin gwamnatin ka yasa yanzu muna iya gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali. An kaskantar da kungiyar Boko Haram, kuma mun yi imanin cewa gwamnatinka zata maganin duk wasu sauran kungiyoyin 'yan ta'adda."

Basaraken ya kara da cewa suna sa ran za a gudanar da babban muhimmin taro domin tattauna tsaron kasa a cikin watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel