Gwamnatin tarayya ta fadi ranar da za ta fara kwaso 'yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin tarayya ta fadi ranar da za ta fara kwaso 'yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin Tarayya ta ce a ranar Laraba za ta fara jigilar kwaso 'yan Najeriya da ke zaune a kasar Afrika ta Kudu sakamakon kashe-kashen kiyayar bakin fata da ya barke kwana-kwanan nan a kasar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin a fara dawo da duk 'yan Najeriya da ke sha'awar dawowa gida nan take.

Jakadar Najeriya a kasar Godwin Adamu, jiya Litinin a Johannesburg ya ce kamfanin Air Peace zai fara jigilar 'yan Najeriya 320 a ranar Laraba kuma wasu za su biyo bayan na farkon.

Shugaban kasar ya bayar da umurnin ne bayan samun rahoto daga tawaga ta musamman da ya turo kasar ta Afirka ta Kudu.

Shugaba Buhari ya jadada cewa akwai bukatar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta dauki kwararran matakai domin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa 'yan kasashen Afirka da ke zaune a kasar.

DUBA WANNAN: Ashura: Mun gano makarkashiyar da gwamnati ta shirya mana - 'Yan Shi'a

Kazalika, Shugaban Hukumar 'Yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri ta ce gwamnatin Najeriya ba za ta bayar da tallafin kudi ga 'yan Najeriya da za su baro kasar ta Afirka ta Kudu ba.

Dabiri-Erewa ta bayar da tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta cigaba da tursasawa gwamnatin Afirka ta Kudu ta biya diyya ga 'yan Najeriya da aka barnata wa dukiyoyi yayin hare-haren na baya-bayan nan.

Tsohon farmanan sakatare na Ma'aikatar harkokin kasashen waje, Ambasada Bulus lolo ya yabawa gwamnati kan matakin da ta dauka na dawo da 'yan Najeriya sakamakon hare-haren duk da cewa ba ita ta tura su kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel