Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun bijirewa yan sanda, sun yi tattakin Ashura a Wuse

Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun bijirewa yan sanda, sun yi tattakin Ashura a Wuse

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi’a ta gudanar da gangamin Ashura a Abuja, inda ta bijirewa yan sanda.

Tattakin Ashura ya kasance wani al’ada da kungiyar ta Shi’a ke gudanarwa a duk shekara a fadin duniya a ranar 10 ga watan Muharram wanda yayi daidai da yau Talata, 10 ga watan Satumba.

Wadanda suka gudanar da gangamin sun hada a maza, mata da kananan yara, sun kuma yi tattakin ne na yan kilomita kadan daga shataletalen Berger zuwa Wuse, sannan suka yi gaggawan kammalawa domin gudun yin arangama da jami’an tsaro.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tattakin wanda aka fara da misalin karfe 8:00 na safe ya dauki tsawon kimanin mintuna 25 sannan ya haddasa cunkoson ababen hawa a cibiyar kasuwancin yankin, amma babu rahoton faruwar wani al’amari.

Ba a samu jin ta bakin kowani kakaki na kungiyar ba yayinda suka ki daga kiran wayoyinsu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Shi’a tace sai tayi gangamin Ashura, ta aika wasiku zuwa ga hukumomin waje

A halin da ake ciki, rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa rikici yan barke tsakanin yan Shi'an da yan sanda a garin Kaduna inda kawo yanzu an bindige mutane uku. Sahara Reporters ta ruwaito.

Wasu da dama sun jikkata. Wani mazaunin Kaduna, Abdu na Abdu ya bayyana mana cewa da sassafe sun ji harbe-harbe a babban titin Nnamdi Azikwe na jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel