Kalli ma’aikatun da gwamnan Bauchi ya tura sabbin kwamishinonin jahar guda 20
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jahar Bauchi dake dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jahar Bauchi, Mohammed Sabiu Baba ta bayyana ma’aikatun da gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya tura sabbin kwamishinoninsa.
Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana sanarwar ta ce: “Biyo bayan rantsar da sabbin mambobin majalisar zartarwar jahar Bauchi a ranar 6 ga watan Satumba, mai girma gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammd ya amince da turasu ma’aikatun da za su yi aiki.”
KU KARANTA: Shugaban kungiyar Malamai ASUU ya yi ma Sanatoci albishir
Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatun da gwamnna ya tura sabbin kwamishinonin sune kamar haka;
Alhaji Nura Manu Soro, ma’aikatan kudi
Dakta Ladan Salihu, ma’aikatan watsa labaru da sadarwa
Dakta Aliyu Usman Tilde, ma’aikatan ilimi
Farfesa Adamu Ahmed, ma’aikatan filaye da sifiyo
Abdulkadir Ibrahim, ma’aikatan ayyuka da sufuri
Jidauna Tula Mbami, ma’aikatan kungiyoyi da cigaban kasuwanci
Dakta Aminu Hassan Gamawa ma’aikatan kasafin kudi da tsare tsare
Hajara Jibrin Gidado, ma’aikatan kula da mata da hakkokin yara
Turaki Mohammed Manga, kwamishinan ayyuka na musamman
Abdulrazak Nuhu Zaki, ma’aikatan kananan hukumomi da masarautun gargajiya
Ahmed Aliyu Jalam, ma’aikatan addini
Modibbo U.A Ahmed, ma’aikatan al’adun gargajiya da bude ido
Sama’ila Ibn Adamu, ma’aikatan noma da cigaban karkara
Barrister Yakubu Bello Kirdi, ma’aikatan sharia
Hamish M. Shira, ma’aikatan muhalli da gidaje
Mohammed A. Sadiq, ma’aikatan ciniki da masana’antu
Umaru Sanda Adamu, ma’aikatan ruwa
Auwal Mohammed Jatau, ma’aikatan kiwon lafiya
A wani labarin kuma, Kotun sauraron korafe korafen zaben gwamnan jahar Kaduna da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2019 ta tabbatar da nasarar da Nasir Ahmad El-Rufai ya samu, inda ta bayyana shi a matsayin halastaccen gwamnan jahar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng