Rufe boda ya dakatar da fasa kaurin man fetir daga Najeriya – Inji shugaban NNPC

Rufe boda ya dakatar da fasa kaurin man fetir daga Najeriya – Inji shugaban NNPC

Shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa matakin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka na garkame dukkanin iyakokin Najeriya na da muhimmin amfani ga tattalin arzikin kasa, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kyari ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda yace rufe boda ya dakatar da badakalar safarar man fetir na Najeriya da ake kaiwa zuwa kasashen nahiyar Afirka.

KU KARANTA: Talauci ya jefa wata budurwa cikin mawuyacin hali bayan saurayinta ya kasa biyan sadakin aurenta

“An samu gagarumar raguwar safarar man fetir daga cibiyoyin man fetir na Najeriya tun daga ranar 22 ga watan Agusta, kuma hakan baya rasa nasaba da kulle iyakokin Najeriya da aka yi da kuma matakan da jami’an tsaro suke dauka don magance matsalar, za mu kawo karshen safarar man fetir.” In ji shi.

A kwanakin baya ma Kyari ya bayyana damuwarsa yadda ake fitar da man fetir na Najeriya zuwa kasar Ghana, inda yace hakan na faruwa ne saboda bambamcin farashin man fetir a Najeriya da Ghana, ma’ana yafi tsada a Ghana.

Shugaban na NNPC ya bayyana cewa yayin da ake sayar da litan mai a N145 a Najeriya, ana sayar dashi a tsakanin N350 – N430 a kasashen nahiyar Afirka, wannan ne dalilin da yasa ake fasa kaurin man fetir.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel