Sunayen shuwagabannin kasashen Afirka 15 da aka musu juyin mulki daga 201 zuwa 2019
Biyo bayan mutuwar Robert Mugabe, tsohon shugaban kasar Zimbabwe, kamfanin dillancin labaru na AFP ta gudanar da wani bincike, inda ta jero sunayen tsofaffin shuwagabannin kasashen Afirka da aka tumbukesu daga ofis tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu.
Ga yadda majiyar Legit.ng ta lisaffa wadannan tsofaffin shuwagabanni da suka gudanar da mulkin kama karya har suka gundiri jama’ansu:
1- 2010
Nijar
A ranar 18 ga watan Feburairu Sojoji suka hambarar da gwamnatin Tandja Mamadou, wanda ya fara mulkin kasar tun 1999.
2- 2011
- Tunisia: Bayan kwashe shekara 23 yana mulkin, jama’an kasar Tunisia sun kifar da gwamnatin Zine El-Abidine Ben Ali a ranar 14 ga watan Janairu.
- Egypt: A ranar 11 ga watan Feburairu tsohon shugaban kasar Misra, Hosni Mubarak ya yi murabus bayan kwashe shekarau 30 a karagar mulku.
- Ivory Coast: Tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya shiga hannun Sojoji a ranar 11 ga watan Afrilu bayan ya hana Alassane Ouattara mulki duk da cewa shi ya ci zaben shugaban kasa na 2010.
- Libya: An kashe tsohon shugaban kasar Libya, Maummar Ghaddafi a ranar 20 ga watan Oktoba bayan kwashe shekar 42 yana mulki.
3- 2012
- Mali: Sojojin kasar Mali sun samu nasarar kifar da gwamnatin Amadou Toumani a ranar 22 ga watab Maris
– Guinea Bissau: A nan ma sojojin kasar ne suka hambarar da gwamnatin shugaban kasa Raimundo Pereira a ranar 12 ga watan Afrilu
4– 2013
– CENTRAL AFRICAN REPUBLIC: Bayan kwashe shekaru 10 yana mulki, Janar Francois Bozize ya arce da kafarsa a ranar 24 ga watan Maris bayan yaki tsakanin Musulman kasar, Seleka Kiristocin kasar, Anti Balaka ya yi kamari.
– Egypt: Shi ma marigayi tsohon shugaban kasar Egypt Mohammed Morsi ya gamu da cin amanan Sojoji na kusa da shi bayan sun yi masa juyin mulki a ranar 3 ga watan Yuli, bayan shekara 1 a kan mulki.
5- 2014
– Burkina Faso: Bayan shekara 27 a kan mulki, shugaba Blaise Compaore,ya tsere daga kasar a ranar 31 ga watan Oktoba sakamakon rikici daya barke a kasar a kokarinsa na neman tazarce.
6 – 2017
– Gambia: Shugaba Yahya Jammeh ya gamu da fushin Sojojin kasashen nahiyar Afirka bayan da yayi kokarin hana zababben shugaban kasar mulki, inda a ranar 21 ga watan Janairu ya fice daga kasar bayan kwashe shekaru 23 yana mulki.
– Zimbabwe: Robert Mugabe ya yi murabus a ranar 21 ga watan Nuwamba bayan shekara 37 a kan mulki
7 – 2018
– Afirka ta kudu: Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu, Jacob Zuma, da ya rike mulki tun 2009 ya yi murabus a ranar 14 ga watan Feburairu.
8– 2019
– Algeria: Bayan daukan tsawon lokaci yana jinya, shugaba Abdelaziz Bouteflika, mai shekaru 82, ya yi murabus a ranar 2 ga watan Afrily, sakamakon zanga zanga da yan kasar suka fara. Shekarunsa 20 a kan mulki.
– Sudan: Shi ma shugaba Omar al-Bashir da ya kwashe shekaru 30 yana mulki ya gamu da fushin Sojiji da suka kifar da gwamnatinsa a ranar 11 ga watan Afrilu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng