Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta ta hanyar yanke masa kai da mazakuta ta bai wa karnukanta suka cinye

Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta ta hanyar yanke masa kai da mazakuta ta bai wa karnukanta suka cinye

- Wata mata ta kashe mijinta ta hanyar yanke masa kai da mazakuta ta kuma bai wa wani karenta ya cinye

- Matar ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda irin cin zarafinta da mijin nata yake yi na tsawon shekara da shekaru

- A take a wajen matar ta bayyanawa 'yan sanda cewa ita ce ta yi wannan aika-aika

Jami'an tsaro sun kama wata mata 'yar kasar Ukraine da ta cirewa mijinta kai, ta kuma yanke masa mazakuta, bayan ta sha fama da cin zarafinta da ake yi na shekaru da dama.

Matar wacce aka bayyana sunanta da Maria, ta dauki mazakutar mijin nata ta bai wa karnukanta suka cinye a kauyensu dake Obariv a arewacin kasar.

Matar mai shekaru 48 ta bayyanawa jami'an yan sanda cewa mijin nata yana gallaza mata na tsawon shekaru da dama, hakan yasa da ta samu dama ta kashe mijin nata.

A lokacin da ta gama wannan aika-aika, sai ta fito kan titi jikinta duk ya jike da jinin mijin nata.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Yan sanda ne suka yi garkuwa dani, suka nemi na basu duka kudin banki na ko su kashe ni - Mawaki Ikechukwu

Maria ta bayyanawa cewa ita ta kashe mijin nata, sannan kuma ta bayyanawa jami'an 'yan sandan ainahin abinda ya faru kafin su saka mata ankwa.

Kakakin rundunar 'yan sandan Vadim Artiukhovich ya ce: "Mai laifin ta amsa laifinta tun kafin mu bar gidan da lamarin ya faru. Ana tuhumar ta da kisan kai, yanzu haka mun kama ta."

Za a yankewa Maria hukuncin kimanin shekaru 15 a gidan yari idan aka kama ta da laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel