Rilwan ya zama Shugaban hukumar bada tallafin karatu na Jihar Kaduna

Rilwan ya zama Shugaban hukumar bada tallafin karatu na Jihar Kaduna

Mun ji cewa Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya nada Hassan Rilwan a matsayin babban Sakataren zartarwa na hukumar bada tallafin karatu da bashi na jihar Kaduna.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin gwamnan jihar Kaduna ta bakin Mai bada shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, gwamnan ya yi wannan nadin mukami ne a makon nan.

Jawabin ya ce:

Malam Nasir El-Rufai ya amince da nadin Hassan Rilwan a matsayin Sakataren zartarwa na hukumar bada tallafin karatu da bashi na jihar Kaduna. Wannan yana cikin tsarin gwamnan na tafiya da Matasa cikin shugabanci, da ba su damar fitowa su koyi aikin gwamnati.”

An haifi Hassan Rilwan a shekarar 1982, kuma ya rike mukamai da dama. Ya rike babban Darektan kamfanin Focal Point Constructions LTD kuma shugaban kamfanin G17 da sauransu.”

Hakan na nufin cewa wannan Bawan Allah da ya samu babban mukami yana da shekaru 37 ne a Duniya. Gwamnan na Kaduna yana cikin masu sha’awar ganin Matasa da Mata a cikin gwamnati.

KU KARANTA: An sace Matashin da ya yi kaurin suna wajen sukar Gwamnati a Kaduna

Rilwan ya yi Digirin farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a bangaren fasaha a shekarar 2005. A 2013 ya samu Digirgir a sha’nin kasuwanci a Jami’ar nan ta Pan Atlantic da ke Garin Legas.

Bayan nan Hassan Rilwan yana da satifiket na kwas iri-iri da ya yi a kasashen waje. Daga ciki akwai wasu daga jami’o’in Amurka da Kenya irin su Northwestern, Harvard da Aga Khan.

Sabon shugaban wannan hukumar ta jihar Kaduna ya na cikin kungiyar nan ta YALI, kuma ya yi aiki a wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta kafa da ya duba sha’anin Almajiranci tun a 2009.

A baya gwamnan na Kaduna ya nada Muhammad Sani Dattijo a matsayin shugaban ma’aikatan fadarsa da kuma Zayd Abubakar a KADIRS. Wadannan duka Matasa ne masu shekaru 39 da 35.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel