Ministan harkokin waje ya bayyana dalilin da yasa wasu gwamnonin Najeriya suka halarci taron WEF a kasar Afirka ta kudu

Ministan harkokin waje ya bayyana dalilin da yasa wasu gwamnonin Najeriya suka halarci taron WEF a kasar Afirka ta kudu

- Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, ya bayyana dalilin da yasa wasu gwamnoni halartar taron zauren tattalin arziki na duniya a ake a kasar Afirka ta kudu

- Ministan yace tuni gwamnonin sun sauka a kasar kafin ma gwamnatin Najeriya ta yanke hukuncin fasa halartar taron

- Ya kara da cewa taron na duniya ne ba wai kasar Afirka ta kudu ba ce ta hada

A ranar Alhamis, ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, yace gwamnonin da suka halarci taron zauren tattalin arziki na duniya a kasar Afirka ta Kudu ba wai sunyi tawaye ne ga hukuncin gwamnatin tarayyar Najeriya ba ne.

Kamar yadda yace, wadannan gwamnanonin da sauran mutanen Najeriya da suka halarci taron sun isa kasar Afirka ta kudun ne kafin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya janye daga halartar taron.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Yayin da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a Abuja, ya nuna cewa taron na kasashen duniya ne wanda ba kasar Afirka ta kudu ta shirya ba.

"An fara taron tuni kafin ma mu kai ga yanke hukuncin janyewa daga halartar taron," inji shi.

Kamar yadda ya ce, "Najeriya ta sanar cewa many an jami'an ta bazasu isa Capetown ba don ta nuna damuwarta akan banbancin da ake nunawa 'yan kasar."

Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya da suka halarci taron zauren tattalin arzikin na duniya a birnin Capetown sun hada da shugaban gwamnonin Najeriya da gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Sauran 'yan Najeriya da suka halarci zauren taron sun hada da tsohuwar ministar ilimi, Obiageli Ezekwesili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel