Bera ya jefa ango a mummunan hali

Bera ya jefa ango a mummunan hali

- Bera ya yi wa ango mummunar barna

- Angon ya jima yana tara kudadensa inda suka kai har dalar Amurka 3,000

- Rahotanni sun nuna angon ya dade yana aiki tukuru don ganin ya tara makuden kudaden

Wani mutum mai shirin angwancewa da masoyiyarsa ya shiga wani hali bayan ya gano bera ya lamushe mishi kudaden da ya jima yana adanawa.

Muhammad Sif wanda ya fito daga yankin arewa maso yamma na Khyber Pakhtunkhwa da ke kasar Pakistan, ya tara kudi har sun kai dalar Amurka 3,000.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Ya adana kudaden ne a cikin wata kwabet ta katako da ke gidansa.

Ana saura kwanaki kadan bikinsa ne ya bude kwabet don dauko adanarsa. Abin mamakin shi ne sai ya ga mafi yawan kudin bera ya cinyesu. Nan take kuwa hankalinsa ya tashi.

Kafofin yada labarai a Pakistan sun shaida cewa Asif ya dauki tsawon shekaru masu yawa yana aiki tukuru don tattara wadannan kudaden amma dare daya bera ya masa ta' asa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel