Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya fadi ba nauyi, Musa Wada ya lashe zaben fidda gwanin PDP
Injiniya Musa Wada ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da aka gudanar yau Laraba, 4 ga watan Satumba, 2019.
Musa Wada, wanda yake kani ga tsohon gwamnan jihar Kogi kuma yayi takara a zaben, Idris Wada, ya lallasa sauran yan takaran inda ya samu kuri'u 748.
Dan tsohon gwamnan jihar Ibrahim Idris, Abubakar Ibrahim, ne ya zo na biyu d kuri'u 710, sai Idris Wada wanda ya zo na uku.
Ga sakamakon zaben:
Musa Wada - 748
Abubakar Mohammed Ibrahim - 710
Capt. Idris Wada - 345
Dino Melaye - 70
Aminu Suleiman- 55
Victor Adoji-54,
Erico Joseph- 42,
AVM Saliu Atawodi (retd.)- 11,
Emmanuel Omebije- 9
Mohammed Shuaibi- 4
Bayo Michael- 2
Jabiru Haruna- 0.
An cigaba da kirgan kuri'un zaben ne bayan rikicin da da ya wakana cikin dare inda wasu yan bindiga suka tarwatsa wajen zaben.
An kammala zaben misalin karfe 1:45 na dare kafin aka tayar da rikici.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng