Wata mata ta zagi Buhari da Osinbajo akan halin ko in kula da suka nuna wajen kashe 'yan Najeriya da ake a Afrika ta Kudu
- Wata mata ta nuna bacin ranta akan halin ko in kula da shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suke nuna akan kisan 'yan Najeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu
- Matar ta yi ta zagin shugaban kasar da matarsa, sannan ta koma kan mataimakinsa Yemi Osinbajo, inda ta ce dole su tashi su dauki mataki
- Ta ce idan har basu dauki mataki ba to tabbas suma rayuwarsu da ta 'ya'yansu ba za ta kare da kyau ba
Wata mata ta nuna bacin ranta akan shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinabjo, inda ta nemi su dauki kwakkwaran mataki akan irin cin zarafin da ake yiwa 'yan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu.
A wani bidiyo da ta sanya a kafar sadarwa ta zamani, matar ta caccaki shugaban kasar da mataimakinsa, inda ta ce dole su tashi tsaye su yi wani abu akan lamarin.
"Bidiyo ne kawai nake yi, yanzu haka 'yan Afrika ta Kudu suna kone gidajen 'yan Najeriya, suna kune gidaje da mutane. 'Yan Najeriya suna kasar Afrika ta Kudu.
KU KARANTA: To fah: An kai gawar wani dan wasan kwallon kafa filin kwallo domin ya buga wasan shi na karshe kafin a binne shi
"Buhari da kai da matarka idan har baku yi wani abu ba to tabbas kuma ba za ku kare rayuwarku da kyau ba. Ba kuma kai daya ba Buhari, har da kai mataimakin shugaban kasa, kai Bayerabe ne, nima Bayerabiya ce.
"Idan kai ma baka dauki mataki ba karshen ka ba zai yi kyau ba daga kai har 'ya'yanka. Idan har baku yi komai a kai ba, kuma baza ku zauna lafiya ba har abada."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng