Fusatattun matasa sun bankawa ofishin MTN wuta a Ibadan

Fusatattun matasa sun bankawa ofishin MTN wuta a Ibadan

Duk da jawaban da gwamnatin tarayya tayi kan hana mayar da martani kan abinda ke faruwa a kasar Afrika ta kudu ta hanyar kai hare-hare kamfanonin yan kasar dake Najeriya, wasu fusatattun matasa sun bankawa ofishin kamfanin sadarwa ta MTN dake Bodija, Ibadan, wuta.

MTN, kamfanin sadarwa mallakin kasar Afrika ta kudu ce kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya.

Matasan sun babbaka ofishin ne misalin karfe 9 na daren ranar Talata.

Hotuna da bidiyoyi sun bayyana kan wannan abu kuma manema labarai sun tabbatar da hakan.

LEGIT.NG HAUSA ta kawo muku rahoton cewa matasa a jihar Legas sun fasa kantin Shoprite da yammacin Talata.

Sakamakon haka jami'an yan sanda suka harbe daya daga cikin matasan kuma an kona motar yan sanda.

Wasu shagunan kasar Afrika ta kudu da aka kai hari jiya sune PEP, MTN, da Shoprite.

KU KARANTA: Kotu ta kwace kujerar wani dan majalisar APC a jihar Ondo

Gwamnatin tarayya ta zayyana wasu matakai da zata dauka domin kawo karshen hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya da wuraren kasuwancinsu a kasar Afrika ta Kudu.

Ministan harkokin kasashen ketare, Mista Geoffrey Onyeama, ne ya bayyana hakan ranar Talata bayan kammala wani taron hadin gwuiwa da babban jakadan kasar Afrika ta Kudu a Najeriya, Mista Bobby Moroe.

Ministan ne ya kira taron a ofishinsa dake ma'aikatar harkokin kasashen ketare a birnin tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel