Matar aure ta gurfanar da malaminta gaban kotun Kano saboda yana nemanta da zina

Matar aure ta gurfanar da malaminta gaban kotun Kano saboda yana nemanta da zina

Yansanda sun gurfanar da wani mutumi mai suna Mas’ud Abdullahi, mataimakin shugaban kwalejin kimiyyar kiwon lafiya ta jahar Kano dake garin Bebeji a kan tuhumarsa da neman wata dalibarsa da zina, wanda kuma matar aure ce.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa a ranar Talata, 3 ga watan Satumba aka yi zaman farko na shari’ar a gaban kotun majistri dake garin Kano, inda Yansanda suke tuhumar Abdullahi da aikata laifuka biyu, wuce iyaka da kuma neman matar aure.

KU KARANTA: Zaben gwamnan jahar Kogi: Yan bindiga sun tashi zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP

Dansanda mai shigar da kara, ASP Yusuf Sale ya bayyana ma kotu cewa a ranar 19 ga watan Agusta ne Nafisa Na’iya wanda take zama a unguwar Hausawa ta shigar da karar Abdullahi zuwa ofishin Yansandan Metro.

A cikin wasikar koke da Nafisa ta aika ma Yansandan, ta shaida musu cewa Abdullahi ya fado cikin gidanta a unguwar Hausawa da nufin nemanta da zina, kamar yadda majiyar Sharp Reporters ta ruwaito Dansanda Sale ya bayyana ma kotu.

Bugu da kari Dansandan ya cigaba da zayyana ma kotu cewa: “A cikin watan Agusta, Abdullahi ya taba aika ma Nafisa sakon kar ta kwana ta Whatsapp irin na soyayya, tare da bukatar ta bashi kanta don ya yi zina da ita, inda ya yi alkawarin bata karin maki don ta haye jarabawarta.”

Daga karshe Dansandan ya karkare da cewa laifukan biyu sun saba ma sashi na 348 da 389 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kano, sai dai da aka karanta ma Abdullahi tuhume tuhumensa, sai ya yi mursisi ya musanta aikata ko daya daga cikinsu.

Ganin haka ta sa Alkalin kotun, mai sharia Aminu Fagge ya bada belin wanda ake kara a ka kudi naira miliyan 1, tare da mutane amintattu guda biyu da zasu tsaya masa a kan naira miliyan daya kowannensu, sa’annan ya dage karar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel