An damke 'Kauraye' 18 a jihar Katsina

An damke 'Kauraye' 18 a jihar Katsina

A ranar Litinin, jami'an hukumar yan sanda a jihar Katsina sun damke wasu matasa maras ji da aka fi sani da 'Kauraye' masu tayar da zaune tsaye a cikin kwaryar jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da wannan labari ga manema labarai inda ya bayyana cewa an samu muggan makamai a hannun matasa. Channels TV ta bada rahoto.

Yace: "Hukumar karkashin jagorancin kwamishanan Sanusi Buba ta samu gagarumar nasara wajen yaki da barandanci da Kauraye da jihar Katsina."

"A karshen maon da ya gabata, hukumar ta samu nasarar kai simame wajen wuraren da kaurayen ke boyewa a jihar."

KU KARANTA: Rikicin jihar Taraba: Kabilar Matasan Jukun sunyi ramuwar gayya, sun yi gunduwa-gunduwa da wasu mutane 5

Daga cikin abubuwan da aka samu hannanunsu sune:

Nadin tabar Wiwi 57

Kwalaben Spirit 250

Sholisho 25

Zarto 1

Guraye da layoyi

Gora, da sauransu.

A bangare guda, Matasan kabilar Jukun a jihar Taraba sun kai ramuwar gayya kan matasan Tibi inda suka yiwa wasu matasa biyar yankan rago a bainar jama'a. Suna zargin matasan na cikin wadanda suka kai hari garin Takum ranar Lahadi, Daily Trust ta bada rahoto.

Bayan kasheshu, matasan Jukun sunyi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu kuma suka bazama kan tituna suna murna da sassan jikinsu.

Wasu mazaunan Takun sun siffanta wannan abu a matsayin abin takaici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel