Rikicin jihar Taraba: Matasan kabilar Jukun sunyi ramuwar gayya, sun yi gunduwa-gunduwa da wasu mutane 5

Rikicin jihar Taraba: Matasan kabilar Jukun sunyi ramuwar gayya, sun yi gunduwa-gunduwa da wasu mutane 5

Matasan kabilar Jukun a jihar Taraba sun kai ramuwar gayya kan matasan Tibi inda suka yiwa wasu matasa biyar yankan rago a bainar jama'a.

Suna zargin matasan na cikin wadanda suka kai hari garin Takum ranar Lahadi. Daily Trust ta bada rahoto.

Bayan kasheshu, matasan Jukun sunyi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu kuma suka bazama kan tituna suna murna da sassan jikinsu. Wasu mazaunan Takun sun siffanta wannan abu a matsayin abin takaici.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, David Misal, ya ce mutane biyar kacal aka kashe lokacin harin.

Yace: "Yan sanda ba da tabbas ko matasan Jukun ne suka kashe wadannan mutane ba saboda babu abinda ba zai iya faruwa ba a irin wannan halin."

KU KARANTA: Kwace kadarorina tauye hakkina ne da kundin tsarin mulki ta bani - Diezani

Mun kawo muku cewa a ranan Lahadi, akalla mutane 12 suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kaiwa al'ummar kabilar Jukun dake karamar hukumar Takum na jihar Taraba.

Yan bindiga sun yi ayari zuwa wasu sassan Takum inda suka harbe mutane da dama, Daily Trust ta bada rahoto.

An samu labarin cewa yan bindigan sun shiga garin Takum ne daga jihar Benue. Wanii mazaunin Takum, Yakubu John, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga da muggan makamai.

Ya ce sun hallaka sama da mutane 12 hakazalika an kashe da dama cikinsu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar DSP David MIsal ya tabbatar da rahoton inda yace jami'an Soji da yan sanda sun yi artabu da yan bindigan kuma sun hallaka da dama cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel