Direban Keke Napep ya maida alabe da gafakar mantuwa ga masu ita a Jos

Direban Keke Napep ya maida alabe da gafakar mantuwa ga masu ita a Jos

Labarin wani Matashi matukin Keke Napep ya na cigaba da yawo a Najeriya bayan da tsabar rikon amanarsa ta bayyana a fili. Wannan abin a yaba ya faru ne a Garin Jos da ke cikin jihar Filato.

Kamar yadda wani Bawan Allah mai suna Isah Miqdad ya bada labari, sun manta da gafakarsu (na’urar komfuta) da kuma alabe (jakar kudi) a cikin Keke Napep amma aka dawo masu da kayansu.

Malam Isah Miqdad ya bayyana wannan ne a kan shafinsa na Tuwita a Ranar Juma'a, 30 ga Watan Agusta, 2019, kuma ya tabbatarwa Legit.ng Hausa wannan a lokacin da mu ka tuntube sa a jiya Lahadi.

Matashin nan mai koriyar riga ya dawo mana da gafaka da alaben mu da mu ka manta da su a cikin Keke Napep dinsa. Bai da wayar salula, amma ya yi ta bi, har ya gano mu, duk da ana sheka ruwan sama”

Miqdad wanda wani aiki ya kai shi Garin Jos ya bada labarin irin sakayyar da su ka yi wa Yaron:

“Mun saya masa sabuwar wayar salula, sannan kuma mu ka ba shi kudi.” Malam Miqdad ya kuma ce: “Bai kamata irin wannan abin alheri ya wuce ba tare da Duniya ta ji labarin Abubakar ba.”

KU KARANTA: Mahaifi na Direba ne – Kakakin Buhari ya fadi tarihinsa

Matashin ya kara da cewa: “Mun je gidan rediyon Unity FM na Jos inda mu ka bada labarin kokarin wannan Bawan Allah. Wannan Matashi, Abubakar Aliyu ya na zama ne a cikin Unguwar Zololo da ke Jos.

Abin burgewar shi ne Keken da Abubakar Aliyu yake haya da shi ba na shi bane na kansa. Amma duk da tsananin ruwan saman da ake yi, bai sa ya tsere da kayan mutane ba, sai da ya gano inda bakin su ke.

Malam Miqdad a shafin na sa na Tuwita ya jawo hankalin Garba Shehu domin su ji labarin wannan Matashi don a karramasa. Mutane da dama dai su na ta rangadawa Abubakar albarka ta ko ina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel