Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)

Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)

Sabuwar amaryar gwamnan jihar Bauchi, Natasha Mariana, ta tare a gidan mijinta, Bala Mohammed, gidan gwamnatin jihar.

Kauran Bauchi ya karbi sabuwar amaryarsa ne a ranar Asabar, 31 ga Agusta, 2019.

Daga cikin kawayen amaryan da suka kawota akwai mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed.

A ranar 26 ga Yuli, 2019 Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya auno sabuwar amarya balarabiyar kasar Labnan amma mazauniyar Najeriya.

Wannan labarin ya bayyana ne ranar Juma'a inda mai magana da yawun gwamnan, Ladan Salihu, ya ce an daura wannan aure a Masallacin Syriya dake Jihar Legas.

Sabuwar amaryar za ta kasance matar gwamnan ta biyu. Kauran Bauchi ne gwamnan Najeriya na uku wanda ya kara aure jim kadan bayan darewa karagar mulki.

Ya bi sahun gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wadanda sukayi aure bayan samun nasara a zabe.

Kalli hotunan:

Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)
Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)
Asali: UGC

Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)
Sabuwar amaryar da Amina
Asali: UGC

KU KARANTA: Kuma dai! Yan bindiga sun kai mumunan hari Takum, jihar Taraba, akalla mutane 12 sun halaka

Sabuwar amaryar gwamnan Bauchi ta tare (Hotuna)
Sabuwar amaryar
Asali: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel