Marigayi Umar Yar'adua, Lukman da sauran mutane 17 da suka jawo aka ci tarar Najeriya biliyan $9 a kotun Ingila

Marigayi Umar Yar'adua, Lukman da sauran mutane 17 da suka jawo aka ci tarar Najeriya biliyan $9 a kotun Ingila

Batun hukuncin da wata kotun kasar Ingila ta yanke na cin Najeriya tarar fiye da Dalar Amurka biliyan $9 ya dauki sabon salo bayan shugaban kamfanin (P&ID) da ya yi karar gwamnatin Najeriya ya bayyaa sunayen mutanen da suke da hannu a kwangilar da aka basu a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Umar Musa Yar'adua.

Michael Quinn, shugaban kamfanin P&ID ya bayyana cewar ya tattauna da tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Umar Musa Yar'adua, tsohon ministan harkokin man fetur, Dakta Rilwanu Lukman, tsohon shugaban kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC), Shehu Ladan da sauran wasu mutane 15 da ke da hannu a kulla yarjeniniyar kafa wata cibiyar sarrafa makamashin iskar 'Gas' tsakanin na hadin gwuiwa tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin PI&D.

Kazalika, ya bayyana cewa ya rubuta takardar tuni zuwa ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, tsohuwar ministar man fetur, Uwargida Diezani Alison Madueke, da kuma tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi bunkasa bangaren man fetur, Dakta Emmanuel Egbogah.

Quinn ya bayyana cewa sun shigar da karar neman gwamnatin ta biya su diyyar $9.6b a kotun kasar Ingila ne a lokacin mulkin Jonathan, kuma sun sanar da Diezani.

Kamfanin PI&D ya shigar da karar gwamnatin Najeriya ne bayan ta gaza sauke nauyin dake wuyanta kamar yadda suke a cikin yarjejeniyar da suka kulla.

DUBA WANNAN: Rushe Masallaci: Ni ba takadar Dalar Amurka bane balle ka kalmashe ka saka a aljihun babbar riga - Wike ya mayarwa Ganduje martani

Ga jerin sunayen mutanen da Quinn ya bayyana cewa na da masaniya a kan yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta shiga da kamfanin PI&D da yake shugabanta.

1. Tsohon shugaban kasa Umaru Yar’Adua

2. Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

3. Tsohon ministan man fetur, Marigayi Dakta Rilwan Lukman

4. Tsohon karamin minista a bangaren sarrafa makamashin iskar 'Gas', Mr. Olatunde Odusina

5. Toshuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke

6. Tsohon mai bawa shugaban kasa shawa a kan bunkasa bangaren man fetur, Dakta Emmanuel Egbogah

7. Tsohon shugaban NNPC, Shehu Ladan

8. Tsofin shugabannin kamfanin NNPC daga 2011 zuwa 2012

9. NNPC

10. NAPIMS

11. Kamfanin 'Addax Petroleum'

12. Neil Hitchcock

13. Engineer Goni Sheikh,(babban sakatare a ma'aikatar albarkatun man fetur)

14. Mrs. Grace Taiga, darektar bangaren shari'a a ma'aikatar albarkatun man fetur

15. Dr. Ibrahim, shugaban tsare-tsare na ma'aikatar albarkatun man fetur

16. Dr. Ogwu Jones (Department of Petroleum Resources)

17. Mr. Taofiq Tijani da Engineer Ikejiani, haiman tsohon Ministan man fetur,

18. Dr. Labi Ajibade, manajan makamashin iskar Gas a hukumar NAPIMS,

19. Dry David Ige, darektan gudanar wa a bangaren 'Gas' da fetur a NNPC

20. Mr. Sunday Babalola na hukumar DPR,

21. Mrs. Uno Adeniji, manajan tsare-tsare a NNPC.

22. Mr. Umar, Manajan makamashin iskar Gas da fetur a NNPC.

23. Mr. Nuhu Tizhe, mai bayar da shawara ga tsohon shugaban NNPC.

24. Mrs. Belgore, mai bawa ministan man fetur shawara a bangaren shari'a.

25. Mr. Debo Spaine na kamfanin Addax.

26. Mohammed Kuchazi (P&ID)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel