Yanzu-yanzu: An hana yan Arewa 123 hana shiga Legas, an tsaresu

Yanzu-yanzu: An hana yan Arewa 123 hana shiga Legas, an tsaresu

Gwamnatin jihar Legas ta hana akalla yan kasuwa 123 daga Arewa da suke kokarin shiga jihar domin neman abinci shiga jihar, an damkesu.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da labarin tsaresu kuma ta garkamesu a shafin yada labaranta na Tuwita. Ta ce laifinsu daya kawai shine suna kokarin shiga jihar Legas.

Jawabin yace: "Jami'an tabbatar da tsaftan jihar Legas a ranar Juma'a ta damke babbar mota dauke da babura 48 da mutane 123 daga jihar Jigawa."

"An kwace mota sakamakon rahoton da aka samu da jama'a wadanda suka bayyana cewa yawan matasan Arewan da yadda suke tafiya na basu tsoro."

"Bayan tsaresu, an garzaya da matasan arewan ofishin hukumar domin gudanar da bincike akansu."

"Daya daga cikin matasan, Shuaibu Haruna, ya ce ya taho daga jihar Jigawa ne domin aiki a Legas da babur dinsa. Ya ce yana mata daya da yaro daya, amma yana neman yadda zai samu kudi domin ciyar da iyalinsa."

"Ana wannan abun al'ajabin karkashin umurnin kwamishanan yanayi da ruwan jihar, Tunji Bello da kwamishanan sufuri, Abimbila Oladehinde."

Kawo yanzu, babu dokar da ta haramta aikin babur a jihar Legas kuma babu dokar da ta hana wani dan Najeriya shiga wata jiha.

Ta wani dalili jihar za ta kama yan Arewa ba tare da sun aikata wani laifi ba?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel