Kaduna: Yan bindiga sun kashe mutane 5, sannan sun kona gidaje da dama a Kaura

Kaduna: Yan bindiga sun kashe mutane 5, sannan sun kona gidaje da dama a Kaura

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane biyar ne suka mutu yayinda aka kona wasu gidaje da dama, a wani hari da wasu yan bindiga suka kai kauyen Zangan da ke Takad a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Mista Bege Katuka, Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta, yace maharan sun kai mamaya kauyen da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Alhamis, sannan suka yi ta harbi ba kakkautawa akan bayin Allah.

“An kashe mutane biyar yayinda har yanzu ba a ga wasu biyu ba. An kuma kona wasu gidaje da dama.

“Mun bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu sannan su yi imani da jami’an tsaro da suka riga suka yi wa yankin kawanya yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya yi wa yan bindiga gargadi da kakkausar murya

Jaridar Daily Trust cewa kauyen Zangan inda mummunan al’amarin ya afku, na raba iyaka da karamar hukumar Riyom da ke jihar Plateau.

A halin da ake ciki, duk wani kokari da ake don tabbatar da lamarin daga kakakin yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya ci tura domin bai amsa kiran waya da sakon da aka tura masa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel