Yanzu Yanzu: Kotu ta kori yaron Dambazau a matsayin dan majalisa, tayi umurnin ba dan takarar PDP takardar cin zabe
Kotun sauraron koraf-korafen zabe na jihar Kano ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta ta soke zaben Shamsuddeen Dambazau, dan tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau, a matsayin mamba mai wakiltan mazabar Sumaila/Takai a majalisar wakilai.
Kotun zaben ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga Surajo Kanawa, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Yadda rigiman ya faro shine, Mista Shamsuddeen wanda bai yi takarar zabe ba amma ya zo na biyu a zaben fidda gwanin APC, ya samu zabenne a lokacin da babbar kotun tarayya na jihar Kano ta watsar da tsohon hadimin Shugaban kasa, Kawu Sumaila, a wani karar kafin zae da akashigar.
Shamsuddeen yayi karar INEC, APC da Mista Sumaila inda ya kalanci tsayar da shi (Sumaila) a matsayin dan takarar APC.
Ya fada ma kotu ta bakin lauyansa, Nuraini Jimoh, cewa Mista Sumaila yayi karar kujerar sanata mai wakiltan Kano ta kudu sannan ya sha kaye a hannun Kabiru Gaya.
Kuma tabbass Mista Sumaila yayi takarar tikitin kujerar sanatan Kano ta Kudu a APC. Ya sha kaye a hannun sanata mai ci, Kabiru Gaya.
KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Dan marigayi Gwamna Audu ya maka Oshiomhole da sauransu a kotu
Daga bisani sai jam’iyyar APC a jihar ta lallashe shi da tikitin dan majalisa mai wakiltan Sumaila/Takai.
APC ce dai tayi nasara a zaben majalisar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng