Tirkashi: An bayyana babban dalilin da yake kawo yawan 'yan luwadi da madigo a Najeriya

Tirkashi: An bayyana babban dalilin da yake kawo yawan 'yan luwadi da madigo a Najeriya

- Wani mawaki mai amfani da shafin sadarwa na Instagram ya wallafa wani rubutu a shafinsa dangane da 'yan luwadi

- Mutumin ya bayyana babban dalilin da ya sanya ake samun yawaitar 'yan luwadi a wannan 'yan shekarun a Najeriya

- Mawakin ya alakanta hakan da matsalar yunwa da talauci a matsayin manyan dalilan da suka sanya mutane ke shiga harkar madigo a Najeriya

Wani mutumi mai amfani da shafin sadarwa na Instagram ya wallafa wani rubutu a shafinsa domin sanar da mutane dangane da wani bincike da yayi da ya sanya ake samun yawaitar 'yan luwadi a Najeriya cikin wannan 'yan shekarun.

Mutumin wanda yake mawaki ne mai suna Jaywon ya bayyana yunwa a matsayin babbar abinda take kawo yawaitar luwadin, duk da dai ya bayyana cewa wasu mutanen suna tsanar gangar jikinsu tun daga lokacin da aka haifeshu, inda suke fatan samun wata hanya da zasu canja gangar jikin nasu.

KU KARANTA: To fah: Abinda nake nema ba shi na gani ba, saboda haka na fita daga Kannywood - Jaruma Halima Abdulkadir

A cewar shi yunwa da talauci sune manyan dalilan da suke sanya yawancin 'yan Najeriya shiga harkar yin luwadi, saboda akwai da yawa daga cikinsu da basa farin ciki da wannan abu da suke, hakan yake nuna cewa akwai wani dalili da ya tilasta su suka shiga wannan harka.

A 'yan shekarun nan dai ana ta faman samun yawaitar 'yan luwadi da madigo a fadin duniyar nan, inda namiji ke neman dan uwanshi namiji haka ita ma mace ta nemi 'yar uwarta mace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel