Gwamnatin tarayya zata fara biyan sabon karancin albashi a watan Satumba

Gwamnatin tarayya zata fara biyan sabon karancin albashi a watan Satumba

- Gwamnatin tarayya zata fara biyan karancin albashi a watan Satumba

- Dama rashin daidaituwa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya ne yasa tuni ba a fara biya ba

- Tun a ranar 18 ga watan Afirilu ne Shugaban kas Muhammadu Buhari yas hannu akan sabon karancin albashin

Shugaban kungiyar kwadago, reshen jihar Ekiti, Olatunde, yace gwamnatin tarayya zata fara biyan karancin albashi a watan Satumba mai zuwa.

Olatunde yace abinda ya kawo tsaiko a fara biyan karancin albashin shine daidaito da ba a samu ba tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta saba take umarnin kotu, Femi Falana

Tun a ranar 18 ga watan Afirilu na shekarar 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a karin karancin albashin tun bayan shekaru 8 da qara karancin albashi.

A ranar litinin, 26 ga watan Satumba, 2019 ne shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Ekiti, Kolapo Olatunde, ya sanar cewa gwamnatin tarayya zata fara biyan sabon karancin albashin a watan Satumba.

Yayi wannan sanarwan ne a yayinda ya zanta da wakilin kwadago na ofishin dillancin labarai a babban birnin jihar Ekiti.

Yace: "Ina tabbatar muku cewa babu abinda zai hana fara biyan sabon karancin albashin na dubu talatin a wata mai zuwa. Gwamnatin zata fara biyan karancin albashin ne a satin farko a watan Satumba."

"Bayan taron zababbu na kungiyar kwadago da mukayi a jihar Kano, mun warware duk wani abu da zai hana biyan sabon karancin albashin. A yanzu dai muna jiran fitowar sakamako."

A yayin da ka tambayeshi takamaiman lokacin da za'a fara biyan karancin albashin, yace: "A watan satumba za a fara biya. Domin kuwa ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya dau zancen karancin albashin da muhimmanci."

A ranar 18 ga watan Afirilu ne Shugaban kas Muhammadu Buhari yasa hannu akan sabon karancin albashin don rage zafi ga ma'aikatan Najeriya; amma fara biya ya gagara.

Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayyar ta karawa duk ma'aikata albashin amma sai gwamnati tace tuni dai tayi kasfi da karin N10,000 ga wadanda albashin nasu ya wuce N30,000.

Hakan ne ya jawo tsaiko gameda fara biyan sabon karancin albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel