Manyan jami’an hukumar kwastam 304 za su yi murabus daga aiki

Manyan jami’an hukumar kwastam 304 za su yi murabus daga aiki

Hukumar yaki da fasa kauri ta kasa ta kammala shirye shiryen yi ma wasu manyan jami’anta guda 304 ritaya sakamakon sun kai shekara 60 a rayuwa, wanda shine shekarun da dokokin aikin gwamnati ya tanadar ma’aikaci ya yi murabus daga aiki.

Rahotanni sun bayyana wasu daga cikin jami’an kuma sun cika shekaru 35 suna aiki, wanda shima tanadi na yin ritaya a cikin dokokin aikin gwamnati a Najeriya. Hukumar ta sanar da wadannan jami’ai shirin ajiye aiki zuwa farkon shekarar 2020.

KU KARANTA: Barayin mutane sun kashe mutane 3, sun yi garkuwa da wasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Daga cikin wadanda ritayan zai shafa akwai kwanturola guda 102 da suka hada da mataimakan manyan kwanturola, DCG, guda biyu, mataimakan manyan kwanturola na biyu, ACG, guda 3, kwanturola 13, mataimakan kwanturola 39 da mataimakan kwanturola na biyu guda 45.

Mataimakan manyan kwanturola, DCG, guda biyu sune: A.A. Dangaladima dake kula da sashin kudi da mulki da kuma Sanusi Umar dake kula da sashin dauka da kula da ma’aikata. mataimakan manyan kwanturola na biyu, ACG, guda 3 sune: Jami’I mai kula da shiyya ta C, Frances Enwereuzor; mataimakin mai kula da sashin kudi da mulki, Bukar Amajam da jami’I mai kula da shiyyar B, Chris Odibu.

Sauran jami’ai masu mukaman kwanturola da za su yi odabo da hukumar sune: Victor Dimka; Florence Dixon; Yusuf Bashar; Francis Adetoye; Gwani M. J; Ogwude L. N; Edede I. E; Abdulahi I. A; Zulkifu A. A; Garba K. U; Loko Y; Angbalaga J. J da Adediran.

A matakin mataimakan kwanturola kuwa akwai Agbo A. H; Abdulrahman T; Salihu M. S; Abubakar M. D; Bello A. N; Chima D. N; Muhammed M; Aliyu D. G; Idris K. I; Namanu A; Zakari N; Ibume R. K; Oyafemi C. I; Waziri S. A; Abioye; T. O; Idris A. I; Muhammed A. B; Ebieme A. U; Adamu S. A; Yusuf S; Adie B. U; Dauda A. Okoloagu D. I; Eneh O. O da Mamu B.

Sauran sun hada da Odwong B. R; Lot-Eburajolo J. E.; Thlama P. W; Umar A; Mustapha I. A; Umoh P. M; Bewaji I. O; Muhammed S. D; Maude A. M; Idris Danladi A. L; Omonoyan O. O; Malah D. A; Tanko S. M da Orekie M.C.

Da yake tsokaci game da sunayen, kaakakin hukumar kwastam, Joseph Attah ya bayyana cewa wannan ba wani sabon abu bane, dama hukumar ta saba shirya jami’anta da zasu yi murabus tare da sanar dasu kafin lokaci ya yi, kuma su kan tafi hutun wata 3 kafin cikar wa’adinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng