Yadda muke hadawa dalibai kwalayen digirin bogi a N2000 kacal

Yadda muke hadawa dalibai kwalayen digirin bogi a N2000 kacal

Wasu masu shaguna a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno sun bayyana yadda suke hadawa mutane kwalin digirin bogi a farashin kudi N2000.

Hukumar tsaron farar hula wato NSCDC a ranar Talata ta bayyana masu irin wadannan shaguna takwas da ta damke wadanda suka kware wajen hadawa dalibai takardun bogi.

Hukumar ta ce ta kasance tana bincike kan yawaitan hada takardun shiga jami'a na bogi, kwalayen didgin bogi, katin zama dan makarantan bogi, risidin kudin makarantan bogi, na jami'o'i daban-daban a Arewa maso gabashin Najeriya, musamman jami'ar Maiduguri.

An damke wadannan matasa tare da takardun bogin da suke hadawa a wasu kasuwa da akfi sani da Post Office.

Kwamandan NSCDC na jihar, Abdullahi Ibrahim, yace: "Sai da hukumar ta kwashi watanni tara wajen binciken wannan abu."

Yadda muke hadawa dalibai kwalayen digirin bogi a N2000 kacal
Yadda muke hadawa dalibai kwalayen digirin bogi a N2000 kacal
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mutane 4 sun hallaka,12 sun bace, yayinda Boko Haram suka kai hari Gajiram

Ya ce yawancin kwalayen digirin bogin da ake hadawa ya shafi bangaren kiwon lafiya domin neman aiki.

Yawancin wadanda aka yiwa wannan kwalin bogin na amfani da su ne wajen aiki da kungiyoyin bada tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Daya daga cikin masu wannan aika-aika, Abubakar Abubakar, wanda yake ikirarin cewa shi ma'akacin jami'ar Maiduguri nemm ya ce wani abokinsa ne ya koya masa aikin.

A cewarsa, suna karban kudi har N1,000 domin yin katin zama dan jami'a.

Wani kuma wanda aka sakaye sunansa yace: "Muna yiwa mutane kwalin Digiri a N2000, yayinda muke yin takardan bankin biyan kudin makaranta N1500 ko N1000."

Ya ce sunada kwalayen digirin makarantu da yawa kuma da su suke amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel