Ja-in-ja: Amurka ta rama matakin da Najeriya ta dauka kan batun yin hatimin shiga kasarta

Ja-in-ja: Amurka ta rama matakin da Najeriya ta dauka kan batun yin hatimin shiga kasarta

- Gwamnatin Amurka ta maidawa Najeriya martani ta hanyar kara kudin hatimin shiga kasar, wato visa

- Karin kudin hatimin 'yan Najeriya kacal zai shafa kamar yadd ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya ya bayyan

- Kasar Amurka din tayi hakanne sakamakon yadda kasar Najeriya ta karawa 'yan kasarta kudin hatimin shigowa Najeriya

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta karawa 'yan Najeriya masu fita zuwa kasashenta kudin hatimin yardar shiga kasahentan, wato Visa.

Sabon kudin hatimin zai fara ne daga kai 'yan Najeriyar da ta yarjewa shiga kasashenta.

Sabon kudin ya farane daga $80 zuwa $110, wanda ya kai N28,000 zuwa N39,000. Zai danganta ne da irin dadewar da mutum ke bukata yayi a cikin kasar.

KU KARANTA: Muna bukatar tallafin gwamnati da cibiyoyin tsaro, iyalan mutanen da akayi garkuwa dasu a jihar Nasarawa

Ofishin jakadancin ya kara da cewa, an kara kudin ne domin yiwa Najeriya kwatankwacin yadda gwamnatin Najeriyar ta karawa 'yan kasar Amurka masu bukatar zuwa Najeriya.

"Dokar Amurka ta bukaci kudin hatimin nata da kuma dadewarta ya danganta da yadda dayar kasar tayiwa 'yan kasarsu, in dai da halin hakan."

Sanannen abu ne cewa Amurka babbar kasa ce dake saukar 'yan Najeriya duk shekara. Sukan je kasar ne aiyuka, karatu, shakatawa da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel