Sama ko kasa, an nemi babban Alkalin kotun tarayya an rasa inda ya shiga

Sama ko kasa, an nemi babban Alkalin kotun tarayya an rasa inda ya shiga

Har yanzu an rasa inda wani babban Alkalin babbar kotun tarayya, Mai Sharia Idrissa Saleh ya shiga tun bayan fitarsa daga asibiti a ranar Asabar 24 ga watan Agusta, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito iyalan Alkali Saleh ne suka sanar da Yansanda halin da ake ciki, inda suka bayyana cewa Alkali Saleh ya sallami kansa daga wani Asibiti da yake jinya a tsakiyar birnin Abuja, amma kuma bai koma gida ba tun ranar,

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya bayyana EFCC da FIRS a matsayin karnukan farautar Buhari

Wani daga cikin iyalan Alkali Saleh daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ya kasance Alkali Saleh yana jinya a wani Asibiti, amma shi da kansa ya fice daga asibitin ba tare da ya sanar hukumar Asibitin ba.

“Mai Sharia Saleh ya kasance yana jinya a wani asibiti ne, amma da kansa ya fita daga asibitin ya tafi ya hau motar Tasi, ya yi gaba ba tare da ya sanar da kowa inda za shi ba, domin hatta hukumar asibitin bata san inda ya yi ba.

“Muna ganin kamar akwai wata babbar matsala dake damunsa, kuma ya kasa gaya ma kowa, amma dai a yanzu haka Yansanda sun fara aikin nemo shi a duk inda yace.” Inji shi.

Shima kwamishinan Yansandan babban birnin tarayya Abuja, Bala Ciroma ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya tabbatar da kaddamar da bincike a kan lamarin, tare da kokarin gano inda Alkalin yake a halin yanzu.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun yi garkuwa da babban likitan asibitin kwararru na Irrua dake garin Irrua na jahar Edo, Dakta Sylvanus Okogbenin, inda suka yi awon gaba da shi a Ramat daje garin Bini.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel