Al’ummar Musulmai sun yi Allah-wadai da rusa babban masallacin juma’a a ribas

Al’ummar Musulmai sun yi Allah-wadai da rusa babban masallacin juma’a a ribas

Shuwagabannin al’ummar Musulmi na jahar Ribas, Fatakwal, sun yi tir da Allah wadai game da rusa wani sabon Masallacin Juma’a na Rainbow Town dake unguwar Trans Amadi, cikin garin Fatakwal.

Shugaban kwamitin Masallacin, Alhaji Musa Tobacco ya bayyana ma jaridar Daily Trust cewa a ranar 20 ga watan Agusta gwamnatin jahar Ribas tare da goyon bayan jami’an tsaro ta rushe Masallacin, inda ta kakkabo fandisho dinsa, tare da sauke katangunsa.

KU KARANTA: Sanata Alu Wamako zai gina katafaren jami’a a jahar Sakkwato

“A shekarar 2008 muka sayo fulatan filayen guda 4 daga hannun Cif Amadi, a shekarar 2009 aka bamu izinin gini, a shekarar 2010 muka gina ginshikan masallacin tare da katangeshi, sai kuma a karshen shekarar 2010 muka sanya tubalin fandishon ginin Masallacin.

“A watan Feburairun shekarar 2010 gwamnatin tsohon gwamna Rotimi Amaechi ta fara rusa Masallacin, hakan tasa Cif Amadi ya shigar da karar gwamnatin gaban kotu, inda a ranar 2 ga watan Nuwambar 2017 kotu ta yanke hukunci tare da baiwa Cif Amadi gaskiya, kuma gwamnatin jahar bata daukaka kara ba, don haka muka sake sabon gini a 2018.” Inji shi.

Gwamnatin jahar Ribas na zargin cewa ginin ya saba ma tsarin inganta birnin Fatakwal ne, kamar yadda hukumar tsara birane ta jahar Ribas ta bayyana, sai dai Alhaji Musa ya roki gwamnatin jahar ta kyalesu su gina wannan Masallaci saboda shine kadai Masallaci a yankin Trans Amadi, yankin da ke da akalla Musulmai 4,000.

Shima shugaban al’ummar Hausawa mazauna yankin, Alhaji Musa Saidu ya bayyana damuwarsa da rusa Masallacin, haka zalika babban limamin Masallacin, Alhaji Haroon Muhammed, ya lissafa sau uku kenan ana cin zarafin Musulmai, “A ranar 29 ga watan Yulio, 16 ga watan Agusta, sai kuma 20 ga watan Agusta.” Inji shi.

Sai dai da majiyar Legit.ng ta tuntubi babban sakataren ma’aikatan watsa labaru na jahar Ribas, Polinious Nsirim game da batun, sai yace ba shi da masaniya game da rusa Masallacin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel