Bayan alfaharin jihar Rivers ta Kiristoci ce, gwamna Wike ya rusa katafaren Masallaci

Bayan alfaharin jihar Rivers ta Kiristoci ce, gwamna Wike ya rusa katafaren Masallaci

Shugabannin al'ummar Musulmi a PortHarcourt, babbar birnin jihar RIvers, sun yi Allah wadai da rusa babban Masallacin Trans-Amadi, inda sukayi kira da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo dauki.

Limanin Masallacin, Haroon Mohammed, ya ce ma'aikatan gwamnatin karkashin umarnin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ne suka dira Masallacin da yan sanda ranar 20 ga watan Agusta domin rusawa.

Ya ce sun yi ikirarin cewa ginin Masallacin bai cikin tsarin gine-ginen jihar RIvers alhalin gwamnatin jihar ce ta tabbatarwa Musulmai filin domin gini a baya.

Yayinda yake kira ga gwamna Nyesom Wike, Imam Haroon yace: "Wannan shine Masallaci mafi girma. Musulman duniya su shaida cewa gwamnatin jihar ce ta bamu damar gina Masallacin. Sau uku kenan ana cin mutuncinmu - An fara ranar 29 ga watan da ya gabata, sannan ranar 16 ga Agusta, sai 20 ga wata ba tare da wani sanarwa ba."

"Yau an hanamu wajen ibada, Bamu son tayar da wani rikici da ma'aikatan gwamnati. Muna son duniya ta rokan mana gwamna ya bamu wajen Ibada, saboda babban Masallacin nan ne daya tilo da al'ummar Trans-Amadi ke amfani da shi."

Gabanin yanzu, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya jaddada cewa jiharsa ba jihar Musulmai bace, jihar Kiristoci ce kuma babu wanda ya isa ya hanashi abinda yaga dama.

Majalisar koli ta shari'ar addinin Musulunci NSCIA ta yi tsokaci kan wannan magana da gwamnan yayi a lokacin inda take jawo hankalinsa cewa a matsayinshi na shugaba, bai kamata ya rika magana irin haka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel