Kuruciya: Wani yaro mai shekaru 13 ya kashe kansa bayan budurwar da yake so a boye ta yi saurayi
An samu gawar wani yaro mai shekaru 13 da ake kyautata zaton ya kashe kansa ne bayan wata yarinya da yake so a boye a makarantarsu ta fara soyayya da wani dalibin daban.
Abokan yaron mai suna Harry Storey sun dauka wasa yake yi bayan ya sanar da su a dandalin sada zumunta na 'WhatsApp' cewa yana tunanin zai kashe kansa bayan ya gano cewa yana da abokin hamayya a son da yake yi wa yarinyar.
Mai binciken mutuwar ban mamaki a garin Oxforshire da ke kasar Ingila, Darren Salter, ya bayyana cewa yaron ya kalli wani fim da a cikinsa wata jaruma ta rataye kanta saboda soyayya a daren washegarin ranar da ya rataye kansa.
Amma, Harry, dan sanda mai gudanar da bincike ya bayyana cewa Harry bai yi niyyar kashe kansa ba a lokacin da ya rataye kansa, ''sai dai ya yi babban ganganci saboda bai yi tunanin cewa zai iya mutuwa cikin dan kankanin lokaci haka ba'' a cewar dan sandan.
Abdulrasheed Maina: Daga karshe, an gano dalilin da yasa Buhari bai sake bawa Dambazau minista ba daga Kano
Andrew Storey, mahaifin yaron, ne ya fara ganin gawar Harry a rataye a saman bene bayan ya dawo daga aiki. Storey ya bayyana cewa da fari ya dauka Harry na tsaye ne a kan wani abu kafin daga bisani ya fahimci cewa ya rataye kansa ne.
Iyayen Harry sun yi matukar dimuwa a kan abinda yaronsu ya aikata, saboda basu yi tunanin zai aikata hakan ba, musamman ganin cewa bashi da wata damuwa ko matsalar tabin hankali.
Su kansu iyayen Harry sun bayyana cewa suna zargin shirin fim din da yaron ya kalla ya taimaka masa wajen kashe kansa, kamar yadda suka shaida wa kotu.
Da take bayar da shaida a gaban kotu, 'yar sanda mai bincike na musamman, Saja Lou Haffernan-Glover, ta sanar da kotu cewa, daga irin shaidun da ta tattaro, bata tunanin Harry ya yi niyyar kashe kansa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng