Farashin wake ya yi rugu rugu a kasuwannin jahar Katsina

Farashin wake ya yi rugu rugu a kasuwannin jahar Katsina

Farashin wake ya fadi warwas daga yadda ake sayar dashi a baya a kan naira 600 zuwa naira 200 a kasuwannin jahar Katsina, kamar yadda rahotom kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu yan kasuwan sun danganta faduwar farashin waken ga shigar sabon kasuwanni, wanda hakan ya karya farashin buhun wake daga naira dubu 24 zuwa naira dubu 8.

KU KARANTA: Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki

Majiyarmu ta zagaya kasuwannin Katsina da suka hada da tsohuwar kasuwa, babbar kasuwa, da kasuwar kofar Marusa, inda ta gano cewa sabon waken yana girma n cikin kwanaki 40 kacal, kuma jama’a sun fi sonshi sakamakon sabo ne daga gona.

Masu sayen waken sun bayyana cewa sun gwammace amfani da sabon wake saboda bashi da kwari a cikinsa, kuma babu sinadaran adanan kayan abinci a cikinsa, ba kamar tsohon wake ba, don haka basu da fargaban cin sa.

Shi ma wani dan kasuwa, Malam Garba Lawal ya shaida ma majiyarmu cewa: “Karyewar farashin ya shafemu sosai, don kuwa ba mu iya sayar da tsofaffin kayan a tsohon farashi, idan kuma zamu sayar a sabon farashi za mu yi babbar asara.”

Shi kuwa Malam Ahmad Musa, cewa ya yi karyewra farashin ya zama kamar rahama ne ga talaka, wanda bashi da isashshen kudin sayan waken a tsohon farashin, amma da karyewarsa, zai iya saya.

Sai dai mataimakin shugaban kungiyar masu sayar da hatsi na jahar Katsina, Alhaji Musa Isah ya bayyana cewa an samu sauki da shigowar sabon wake, amma ya gargadi jama’a da kada su ajiye shi ya dade, saboda bashi da kwari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel