Mu na son aure, mata masu aiki a asibitoci sun koka a kan rashin samun masoyashin

Mu na son aure, mata masu aiki a asibitoci sun koka a kan rashin samun masoyashin

Wata kungiyar mata masu aiki a asibitoci (Nurses) a kasar Ghana sun yi kira ga maza da su fito domin neman aurensu.

Kyawawan 'yammatan da gwamnatin kasar Ghana ta dauka aiki a asibitoci sun koka a kan rashin samun kulawa daga wurin maza balle ma har ta kai ga maganar aure.

A wata hira da suka yi da wata jaridar kasar Ghana (Ghface.com), 'yammatan, wadanda dukkansu sun isa aure, sun bayyana cewa a shirye suke su karbi duk wanda ke son aurensu hannu bi-biyu tare da bayyana damuwa da tsoronsu a kan yadda maza ke nuna 'halin ko in-kula' a kansu.

"Mu na son aure, kuma a shirye mu ke, amma maza basa tunkarar mu domin neman auren mu. A shirye muke mu amsa bukatar duk wani namiji da ya fito da gaske domin neman auren mu. Kar maza su ji tsoro, za mu karbi duk mai son auren mu hannu bi-biyu. Ba sharholiya ce a gaban mu ba yanzu, mun girma, don haka aure kawai muke so," a cewar 'yammatan.

DUBA WANNAN: Asiya da Atika, kwararrun masu garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kebbi

Da suke kokarin amsa tambayar dalilin da yasa maza basa son auren 'yammata masu aiki a asibiti, 'yammatan sun bayyana cewa maza da yawa na gudun aurensu ne bisa kuskuren zargin cewa mata masu aiki a asibiti basu da kunya, kuma zasu iya cin amanar namiji cikin sauki saboda yanayin aikinsu.

"Maza da yawa na zargin cewa matan da ke aiki a asibiti basu da kunya kuma sangartattu ne, amma hakan ba gaskiya bane. Mun dauki aikin mu da muhimmanci, mu na matukar girmama aikin mu, lamarin da wasu mazan suke dauka a matsayin rashin kunya," a cewarsu.

Wasu kuma daga cikin 'yammatan sun bayyana cewa maza da yawa basa son auren matan da ke da aiki, aiki wuri 'ya mace na firgita wasu mazan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel