Yan Boko Haram sun kona ofishin INEC a harin Gubio

Yan Boko Haram sun kona ofishin INEC a harin Gubio

Dubunnai sun gudu daga muhallansu yayinda wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka kai hari garin Gubio da Magumeri dake Arewacin jihar Borno a daren Laraba, Daily Trust ta bada rahoto.

Yan ta'addan sun dira garin Gubio, hedkwatar karamar hukumar Gubio misalin karfe 5:40 na yamma kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Wani jami'in sojan 5 Brigade dake Damasak ya bayyanawa The Cable cewa yan ta'addan sun kasance a garin Gubio tun tsawon watanni ukun da suka gabata tun lokacin da aka kwashe sojoji daga yankin.

Yace: "Babu soja a Gubio, shi yasa suka sami damar shiga. Sun kona ofishi INEC da wasu gidaje,"

"A yanzu a nike muku magana, an tura sojoji daga bariki kuma sun batakashi da yan ta'addan".

Yan Boko Haram sun kona ofishin INEC a harin Gubio
Yan Boko Haram sun kona ofishin INEC a harin Gubio
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Hankali ya tashi, Yan Boko Haram sun kwace garin Gubio da Magumeri

Wani dan jarida, Jack Vince, ya bada irin wannan labari.

Yace: "Kimanin makonni biyu kenan babu sojoji daga Damasak wajen iyakan Najeriya da Nijar zuwa unguwata a Maiduguri, Magumeri, Kareto, Gubio da sauransu."

"Ana kwace Gubio, sojoji suka gudu zuwa Damasak da Maiduguri inda suka bar wurare babu kariya."

Wata majiya ta bayyanawa The Cable cewa sojoji sun janye daga garin ne saboda mazauna garin basu baiwa sojoji hadin kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel